Min menu

Pages

Allah ya kiyaye:- Rokar da china ta harba ta fado wannan gurin

 Rokar da china ta harba ta fada wani guriA yan kwanakin nan ko ina ya cika da labarin cewar kasar China ta harba wata roka wadda ta bace.


Saidai ko ina mutane na cike da jimamin inda zata fada domin idan har ta fada guri to kuwa ana tunanin samun asara mai yawa na daga rayuka da sauran abubuwa.


Da fari an fara yada jita jitar rokar kan iya fadawa a Abuja babban birnin kasar Nijeriya wanda hakan yasa mutane da yawa cikin su ya duri ruwa.


To jiya da akayi bincike sai akaga rokar baza ta fada a Abuja dinba amma dai zata iya fadawa ko ina ne.


Sai yau kuma da safe ake jin labarin rokar ta fada cikin wani kogi na kasar India.


Saidai har yanzu babu wani rohoto daya nuna irin barnar da rokar tayi

Comments