Min menu

Pages

ABIN MAMAKI:-Ya cakawa matarsa wuka, ya cire mata ido sannan ya kashe kansa

 


Wani abin mamaki da al'ajabi ya faru inda wani mutumi ya yankewa matarsa gashin kanta sannan ya cire mata ido daga karshe kuma ya kashe kansa.


Koda wanne lokaci muna cin karo da labarai masu bada mamaki matuka, to amma da wuya in mun taba karanta irin wannan labarin ko mun taba sauraron labari mai kama dashi.


Ta inda mutum zai kashe matarsa da kansa anya kuwa akwai soyayya cikin wannan zaman nasu?


Majiyar ta rawaito masoyan guda biyu sunyi kaura daga inda suke zaune zuwa wani guri da yake lekki sati uku kafin wannan abin ya faru.


A ranar lahadi da abin zai faru makotan da suke kusa da gidan miji da matar sunji an saka kida mai karfi wanda harya fara takurawa makotan hakan yasa wasu da dama suka tafi gidan domin su sanar dasu cewa su rage karar kidan.


Lokacinda suka shiga gidan sai sukaga bangaren nasu a rufe hakan yasa suka tafi bangaren da yaran gidan suke anan suka samu wata yarinya suka fada mata ita kuma kai tsaye saita tafi ta fara bugawa domin su bude amma shiru.


Bayan yarinyar da kuma makotan sun gaji da bugawa sai suka yanke shawarar karya kofar su shiga hakan kuwa akai suka balla kofar suka shiga.


Lokacinda suka shiga sai suka dinga ganin wukake a jefe da jini saida suka shiga daki anan suka ga mata da mijin a kwance cikin jini sun mutu.


To amma har yanzu an kasa gane dalilin mutuwar tasu.


Comments