Min menu

Pages

Ya fille kan kakarsa sannan ya dauki kan ya kai har gurin yan sanda

 Ya sare kan wata tsohuwar kakarsa sannan ya kaiwa yan sanda har office dinsuWani fusataccen saurayi yayi karfin halin fillewa kakarsa kai sannan ya dauki kan ya wuce har ofishin yan sanda dashi.


An cika da mamaki lokacin da yan sanda suka ga wani saurayi dauke da bokiti ya nufo inda suke zaune.


Yana zuwa yace musu gashi, abin ya basu mamaki domin sun dauka wani abu ne ko kuma mai tallan abinci ne, suka tambayeshi menene a  ciki ba tare da fargaba ko tsoro ba yace kaine a ciki.


Cikin mamaki yan sandan suka ce kai kuma, kan menene?


Kan kakata ne saurayin yace musu ba tare da yaji tsoro ba sannan ya bude botikin kai tsaye kuwa yan sandan sukai arba da kayin wata tsohuwa yar kimanin shekaru saba'in.


Cikin sauri suka kama saurayin tare da garkama masa ankwa sai unguwar da saurayin yake.


Suna suna zuwa suka shiga gidan ai kuwa sai sukaga gangar jikin tsohuwar a yashe duk jini ya bata gurin.


Makotan dake kusan gidan dama yan unguwar sun nuna basu san haka ya faru ba sannan mutane da yawa sun nuna cewa tsohuwar tanada kirki sosai.


Wannan yasa wasu daga cikinsu suka fusata suka iyo kan matashin dake hannun yan sandar domin su gabatar masa amma yan sandan suka shiga tsakani.


Wannan al'amarin ya faru ne a kasar kenya unguwar Nyalenda.


Har yanzu dai yan sandan suna rike da saurayin domin suyi bincike su gano dalilin da yasa wannan saurayin aikata wannan mummunan aiki akan kakar tasa.

Comments