Min menu

Pages

Wata mata ta jefar da wani jariri sabuwar haihuwa a Wani bandaki a cikin kasuwa

 Wata mata ta jefar da wani jariri sabuwar haihuwa cikin wani bandaki dake cikin kasuwa.Wani mazaunin gurin shine ya sanar da faruwar wannan lamarin, yace yaje zaiyi bayan gida kusa da bandakin shine yaji kukan jaririn.


Daya duba sai ya ganshi kusa da inda mutane ke yin kashi a cikin bandakin.


Wannan al'amarin ya faru ne misalin karfe takwas da rabi na dare.


Matar da har yanzu ba'a gano ko wace ce ba ta jefar da jaririn cikin bandaki wanda mutanen kasuwa ke amfani dashi sannan ta gudu a kauyen Bako can wajen kwali dake Abuja.


Mutumin daya ga yaron yayi saurin sanar da mutane wanda daga karshe an dauki yaron an wuce dashi wani asibiti wanda daga karshe shugaban karamar hukumar na kwali shine ya dauki nauyin kula da jaririn.

Comments