Min menu

Pages

Na kamu da kaunar wani saurayi a facebook daga karshe na ziyarce shi amma dubi abinda yamin

 Na kamu da kaunar wani saurayi a facebook wannan tasa na ziyarce shi amma dubi yadda yamin.Sunana blessing kuma duka shekaruna basu gaza ashirin da hudu ba sannan ina karatun lafiya a university yanzu haka ina level 3.


Saurayin ya neme ni dana zama abokiyarsa a facebook ni kuma na yarda na amince har muka fara magana bayan na duba profile dinsa naga ya hadu kuma yayi.


Bayan dan lokacin da muka dauka muna magana can wata rana sai yace dani yana sona ni kuma na amince saboda ya hadu matukar haduwa.


Mun fara soyayya daga nan yake sanar dani a Enugu yake daga karshe muka yanke akan cewa zan kai masa ziyara na aminta da hakan shine ya turamin kudi akalla dubu talatin da biyar domin nayi kudin mota.


Wannan kudin daya tura ya sake tafiya dani domin na yadda saurayin nawa mai kudi ne mu kuma yan mata muna son saurayi mai kudi.


A ranar da naje garin na tarar dashi a yadda yake hadadde ne to amma maimakon ya saukar dani a gidansu saiya kaini wani daki a hotel.


Bayan mun shiga mun zauna ya kawo min wani lemo banyi masa musu ba na karba na fara sha ai kuwa take naji jiri yana daukata.


Bayan na kwanta shine daga karshe ya iyo kaina yana neman kusantar inda nake na kauce ya sake iyowa kaina shine nai masa tsawa to wai sai yake cewa ai ya kashe kudi masu yawa a kaina..


Daga karshe dai mukai baram baram dashi.

Comments