Min menu

Pages

Innalillahi wa'inna'ilaihirrajiun sun sake kullowa Pantami wani sabon sharrin

 Sun sake kullowa Sheikh Isah Ali Pantami wani sabon makirci a kokarin su na ganin bayan shiYanzu haka wani tsohon Farfesa a jami'ar Kaduna mai suna Samuel Achi ya yi ikirarin cewa Sheikh Isah Ali Pantami yana da hannu dumu-dumu a kisan yaronsa a shekarar 2004 a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi.


Tsohon Farfesan ya bayyana cewa an kashe yaronsa ne a lokacin da Sheikh Pantami yake limami a masallacin jami'ar ta ATBU, a lokacin da yaronsa ya yi rabon wasu takardu wadanda akace suna dauke da zagin fiyayyen halitta Annabi Muhammadu da kuma addinin musulunci.


A cewar sa, an kashe yaron nashi ne ta hanyar shake shi a wani guri a cikin jami'ar.


To sai dai babban abin tambaya a nan shine; Miyasa wannan tsohon Farfesa arne bai fito ya bayyana hakan ba tun a shekarar 2004 sai yanzu a daidai wannan lokaci da ake neman 6atawa malam da suna?


Hakika wannan shine zai tabbatar muku da cewa alakanta malam da kungiyoyin ta'addanci na duniya kullallen abu ne wanda aka tsara.


Sai dai sun bi duk wasu hanyoyi don ganin an same shi da wani laifin ta'addanci amman basu yi nasara ba, shine wannan tsohon arne ya fito da wannan magana domin ganin sun cimma burinsu akan wannan bawan Allah.


To muna rokon Allah ya taimake shi ya tsallake wannan sabon tarko kamar yanda ya tsallake saura.Comments