Min menu

Pages

An fara takun saka zakanin Dangote da BUA

Kamar an fara takun saka tsakanin yan kasuwar guda biyu BUA da kuma DANGOTEShahararrun 'yan kasuwan nan na Afrika kuma 'yan asalin jihar Kano, Alhaji Aliko Dangote mai kamfanin Dangote Group da Alhaji Abdulsamad Isiyaka Rabi'u sun sa zare, yayinda Aliko Dangote ya rubuta wa Gwamnatin Tarayya zungureriyar wasika yana so Gwamnatin ta rufe babban kamfanin BUA na Sikari dake birnin Fatakwal din jihar Ribas.


Wasikar wanda Dangote ya sanyawa hannu da kansa, ya aike wa ministan masana'antu na Nijeriya.


Kwanan nan dai Abdulsamad ya bayyana wa manema labarai a jihar Kano cewa duk wani dillalin da yake hulda da kayayyakinsu ka da ya sake ya kara farashin kaya cikin wata azumi mai zuwa, idan ba haka ba zai kwace lasisin sayar masa kaya.

Comments