Min menu

Pages

Yazo bautar kasa NYSC kauyen mu amma kullum saiya doke ni amma daga karshe ga abinda ya faru inji wata budurwa

 Yazo bautar kasa NYSC kauyen mu amma kullum saiya doke ni amma daga karshe ga abinda ya faru inji wata budurwa.Wani dan bautar kasa da yazo kauyen mu kullum saiya dokeni saboda wai ina zuwa a makare.Budurwar dake bada labarin tace abune mai matukar wahala taje makarantar nan ba tare da malamin ya mata dukan makaranta.


A yadda tace ni da safe dole na a gida sai nayi aikace aikace kafin na samu na tafi makaranta wanda hakan yakansa naje a makare, shi kuma ya doke ni duk da cewa ni bana fada masa abinda yake sani makara ko ya tambaye ni a cewar budurwar.


Wata rana bayan nazo a makare kuma ya tambayeni dalilin makarata ban fada masa ba saiya rabu dani bai doke ni ba kamar yadda ya saba saida muka tashi a makarantar bayan kowa ya tafi gida da jimawa sai gashi a gidan mu.


Bayan sun gaisa da mahaifiyata shine yake cewa me yasa kullum saina makara.


Mahaifiyar tawa sai tace dashi ni kadai ce a gidan kuma da safen nakan tayata aikin dafa abincin da zata fitar kasuwa domin tana samun dan kudaden da za tana saya min abubuwan da zanyi amfani dasu kuma da yar wannan sana'ar take daukar duk wata dawainiyar gidan harda kudin karatu na da sauran abubuwa domin mahaifanta ya rasu kuma babu masu tallafa mana dan haka take makara inji mahaifiya ta.


To tun daga ranar ya daina dukana koda na makara kuma daga karshe shine ya daukin nauyin komai na gidan mu in takaice muku zance yanzu shine zai aure ni nanda wasu lokuta a cewar budurwar.


Duniyar labari taku ce!

Comments