Min menu

Pages

Yan Sanda sun cafke wata mata bisa laifin yiwa yaro fyade a gidan iyayensa

 Tirkashi! An kamata bayan ta yiwa wani yaro fyade a gidan iyayensaAn kama wata mata a kasar Zimbabwe bisa zargin yiwa wani yaro dan shekara goma sha uku (13) fyade.

An kama wannan matane a ranar talata, matar wadda akace daga rukunin gidajen Greendale take Wanda mafi akasarin mutanen wajen masu hannu da shuni ne. 


Matar an kamata ne a gidan su yaron da ake zargin ta aikatawa faden dake a Houghton park.

Matar wanda ba'a gama tantance sunan taba tayi kokarin kare kanta a wajen yan sandan da sukaje suka kamata ta hanyar nuna musu kororan roba a matsayin hujjarta tana mai cewa tayi amfani da abin kariya wajen saduwa da yaron.

Mai magana da yawun yan sanda mataimakin kwamishinan yan sanda Paul Nyathi ya tabbatar da kama matar ya kuma ce har sun fara bincike.

"Yan sandan Zimbabwe zasuyi bincike akan matar da aka kama bisa zargin kwanciya da yaro  maras galihu a Houghton park" Inji mataimakin kwamishinan yan sanda Paul Nyathi.

"Muna Bincike tare da bibiya domin mu samo asalin yadda al'amarin ya faru idan aka kammala zamu fitar da cikakken bayanin yadda komai ya faru" a fadar mataimakin kwamishinan. 

A yayin tattaunawa da matar da har yanzu ba'a gama tantance sunan taba tace yaron shine Wanda ya dauki waya da Kansa ya kirata har gida domin ta sadu dashi.

".Mun sadu ni da yaron nan cikin hanyoyin kariya banga dalilin da zaisa a rika yimin kamar wata barauniya ko yar fashi ba"  matar ta fada Cikin zubda hawaye a lokacin da yan sanda suke tusa keyarta izuwa cikin motar su.

Mahaifiyar wannan yaro ta bayyana cewa ta kama matar tanayin fade ga danta bayan da ta dawo cikin gidan daga wani wajen data fita, ta kuma kara da cewar ina ganin matar na tabbatar matar karuwa ce.

Matar dai an kaita ofishin yan sanda na waterfall domin tsareta kafin a kammala bincike.

Comments