Min menu

Pages

Wani abu yasa ya kashe yarsa yar shekara hudu a Jihar Jigawa

 Wani magidanci ya kashe yarsa yar shekara hudu har lahira.Al'amarin ya faru ne a Jihar Jigawa dake Nijeriya.

Ba wani da yake da damar kashe wani koda dansa ne ko kuma ba dansa bane a wannan zamanin, wannan abinda ya faru rashin adalci ne akan yara, da har mahaifi zai iya kashe yarsa daya haifa. Kodan tsoron talauci ko wani abu daban.

Wani abu ya faru a jigawa da ya bewa mutane mamaki inda aka kama wani daya kashe yarsa.


An samu labarin wani magidanci ya kashe yarsa yar shekara hudu ta hanyar binneta da ranta a cikin dakinsa.


Dan haka shima an yanke masa hukunci ta hanyar rataya kamar yadda Wani alkalin  wata kotu dake zamanta a Ringim ta sanar da wannan hukuncin.


Malam Nasiru hamisu shine mai gidan daya kashe yar tasa mai suna zainab ta hanyar binneta da ranta a dakin bacci.


Inda alkalin kotun ya fitar da cewa shima an yanke masa hukunci ta hanyar rataya.


Mutanen da suka halacci zaman kotun sun hada da wani babba dake aiki a asibitin garin Ringim din da kuma mahaifiyar yarinyar tare da wasu jami'an gwamnati da aka turo daga jihar.

Comments