Min menu

Pages

Sheik Gumi yayiwa sojoji bayani dalla dalla

 

Malam Abubakar Mahmud Gumi yayiwa sojoji bayani dalla dalla akan kalaman da yayi a kansuBa bata sunan sojoji nake so nayi ba fahimtar maganata ne ba suyi ba.


Shehin malamin nan da yake shiga jeji domin yin sulhu da yan bindinga ya baiyanawa sojoji cewar shifa ba bata musu suna yake ba ko son aga laifinsu.


Yayinda yace shi kalamansa ga gurbatattu daga cikin sojojin da suka bata kasa yake.


To saidai sojojin sun fito sun gargadeshi bisa kalaman da yake na cewa furucinsa na iya tada husuma a kasa.


Saidai malamin yace sam basu fahimci zancen nasa daidai ba.


Yace gura gurbin da yace akwai cikin sojoji yana nufin daga 2010 ne zuwa 2015.


Wanda mutanen dake rike da madafun iko na cikin sojojin suka rinka bari abubuwa sunata faruwa.


Sannan malamin yace shi yanada dangantaka mai karfi tsakanin sa da sojojin tunda farko dan haka har yanzu babu abinda ya sauya.

Comments

1 comment
Post a Comment
  1. Mai gida gaskiya yayi sai dai ni Ina blogger a free Amma har yanzu AdSense Basu karba shin ya zanyi na bari ko na ci gaba don Allah ka ba ni shawara

    ReplyDelete

Post a Comment