Min menu

Pages

Iyayen daliban da aka sace sun nemi gwamnatin kaduna ta amince su biya kudin fansa domin a sako yayansu

 Muna bukatar gwamnatin Kaduna ta amince da batun kudin fansa inji iyayen daliban da aka saceIyayen daliban makarantar da aka sace na kaduna sun roki gwamna Malam Nasiru El-rufa'i daya amince da kudurin yan bindinga na biyan kudin fansa domin a sako musu da yayansu.


Iyayen daliban sun sake rokar gwamnatin da tayi hakuri suyi sulhu da yan bindingar domin a sake musu yayansu.


Tunda aka sace daliban dai hankalin iyayen nasu ya tashi kuma suke zaman dardar tun bayan da gwannan yace shi bazai nemi sulhu da yan bindingar ba sannan kuma bazai biya kudin fansa ba.


To saidai iyayen daliban da aka sace na makarantar fcfm sun roki gwamnan da yayi hakuri ayi sulhu da yan bindingar.


Sunce koda yaushe hankalinsu baya kwance idan sun tuna yan yayansu basa tare dasu.

Comments