Min menu

Pages

Hukuncin da akai ma Manajan da ya Satar ma Dangote $ 32,000

 


Wannan shine Hukuncin da aka yanke ma Manajan Kamfanin Dangote da aka kora, saboda satar zunzurutun kudi har $32,000....Babbar kotun jihar Legas da ke a ikeja ta daure Raymomd Akanolu shekaru dai dai har bakwai a kurkuku saboda badakala da halin bera da yayi na karkatar da zunzurutun kudi har dala dubu talatin da biyu ($ 32,000) lokacin da yake aiki a mtsayin babban Manajan Dangote.
Wata sanarwa da kakakin yada labarai na hikimar EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar a ranar talata yace mutum uku aka yanke ma wannan Hukuncin da shi Akanolu sai Mojisola Aladejobi sai wani da ake kira da Balogun Alaba.An gurfanar da su ne a gaban mai shari'a S S Ogunsanya, aka tuhume su da aikata lafuka har guda biyu da ya hada da kokarin satar kudi har $ 32,000.To sun dai nuna cewa ba su aikata wannan laifi da ake tuhumarsu dashi ba, wannan dalilin yasa kotun data shari'ar gadan gadan don gano gaskiyar lamarin.

Masu gabatar da kara S.O Daji Babatunde Sonoki sun kira masu shaida tare da mika ma kotu wasu kofin takardu da suke kunshe da tabbacin lafin ga wadanda ake tuhuma.
An samesu dumu dumu da laifin kara kudin inshorar wani jirgin kamfanin DIL da sukai ma aringizon kudi har dala 32,000 kan jirgi mai Lamba 52 - DGN.
Wannan laifi dai ya saba dokokin kasa da na jaha baki daya. Don haka aka yanke masu Hukuncin zaman gidan yari har na shekara bakwai.


To Allah Ya kyauta Yasa mufi karfin zuciyarmu Ameen.

Comments