Min menu

Pages

Darakta Ashiru na goma ya fara samun lafiya

Allah abin godiya daraktan fina finan hausa daya jima da samun tabin hankali ya fara samun sauki Tsohon daraktan finafinan hausa, Ashiru Nagoma ya fara samun sauki


Yanzu haka shahararren tsohon daraktan shirya finafinan Hausa a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood Ashiru Nagoma ya fara samun sauki na jinyar da yake fama da ita na ciwon tabin hankali.


Jama'a idan zaku tuna watanni biyu da suka wuce an tafka muhawara akan shi saboda irin halin da ya shiga na rashin lafiyar kwakwalwa(Tabin-Hankali) cewa jaruman masana'antar Fim ta Kano basu kyauta ba barin shi a wannan hali na tabin hankali ba tare da sun dau matakin yi masa magani ba.

Inda wasu kuma ke nuna cewar basu da laifi tunda dai sunyi bakin kokarinsu.

To sai dai Gidauniyar @Creativehelpingneddyfoundation ta dauki nauyin kai shi Asibiti tareda bashi kulawa ta musamman, kuma cikin ikon Allah an fara samun nasara sosai


Muna rokon Allahu ya bashi lafiya.

Comments