Min menu

Pages

An kusa kawo karshen ta'addanci da matsalar tsaro a arewa

 Indai matsalar rashin tsaro ne da kuma ta'addancin dake faruwa a arewa ne to sun kusan zuwa karshe..Wani babba kuma jagoran bataliyar sojoji na daya janar Dan Juma Ali Keffi shine yai wannan maganar.


Yace Insha Allahu indai batun ta'addanci ne da ake fama dashi a yankin arewa ne to mutane su kwantar da hankalinsu ya kusa zuwa karshe.


Kwamandan bataliyar sojojin na daya yace suna nan suna shiri domin kawar da duk wasu yan ta'adda da suka takurawa yankin arewa..


Sannan ya kara da cewa abinda sojoji suke bukata shine yan kasa su tashi tsaye wajen tayasu da addu'a domin ganin an shawo kan matsalar tsaron a kasa.Comments