Min menu

Pages

ZAN KUNYATA MALAMAN KANO A IDON DUNIYA CEWAR ABDULJABBAR

Zan halarci mukabalar da aka shirya mana da malaman Kano, Abduljabbar Kabara Abduljabbar Kabara ya nuna jin dadinsa a kan ranar da Ganduje yasa na mukabalarsa da malaman Kano - A cewar Abduljabbar, ya matukar jin dadi yadda gwamnan ya bashi damar kare kansa kuma zai samu halarta - Kabara ya tabbatar da cewa dukkan koyarwarsa da wa'azinsa yana baiwa Annabi kariya ne, akasin zargin da ake masa Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi martani a kan wasikar da gwamnatin jihar Kano ta aika masa na ranar da za a yi mukabala tsakaninsa da malaman Kano. Ya tabbatar da cewa zai halarta.


Malamin a wata wasika da ya aikewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ce zai halarci mukabalar kuma ya yi godiya ga gwamnan a kan damar da ya bashi domin kare kansa. Idan za mu tuna gwamnatin jihar ta saka ranar Asabar, 7 ga watan Maris domin mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da sauran malaman jihar, Daily Trust ta wallafa. Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, a wata takarda a ranar Lahadi ya ce daga  Abduljabbar da malaman Kano duk an basu wasikar wacce ke bayyana ranar mukabalar. Amma kuma Abduljabbar ya ce dukkan koyarwarsa da wa'azinsa yana yi ne don baiwa nagartar Annabi Muhammad kariya ba kamar yadda wasu mutane ke zarginsa ba.  

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments