Min menu

Pages

 Ta yadda jami'an tsaro suka gaza



Lawyer kuma tsohon ministan matasa da wasanni na kasa Hon. Solomon Dalung ya bayyana cewa jami'an tsaron na Najeriya sun gaza wajen kawo zaman lafiya. 


Ya nuna damuwarsa karara kan yadda hare-haren ta'addanci ke karuwa babu kakkautawa a yankin arewacin Najeriya, yace hakan duk yana faruwa ne a bisa sakacin jami'an tsaro.

Yayin da ake ci gaba da sace-sacen dalibai da malamansu a arewacin Najeriyar hakan ya diga ayar tambaya akan yaushe ne tsaro zai inganta ga rayuwar al'umma kamar irin dalibai da malamansu Wanda matsalar take ta kara shafa babu kakkautawa ba tare da sunji ba ko gani kawai sai azo a sacesu.


 A kwanakin bays wasu yan bindiga a jihar katsina sun sace dalibai a wata sakandire dake a karamar hukumar kankara, Wanda sai daga bays aka samu yaran suka kubuta.

Kwatsam ana zaune kuma wata sabuwar satar dalibai ta faru a wata kwaleji kimiyya dake  kagara dake jihar neja, wannan al'amari yayi matukar girgiza zukatan mutane musamman dalibai da kuma iyayensu haka kuma ya kara firgicin da ake dashi na rashin tabbas akan tsaro.

Solomon Dalung yace jami'an tsaro gaba daya sun gaza wajen daukar darasi akan abin daya faru da daliban kankara, maimakon su dauki matakin dazai hana sake aukuwar wannan al'amari sai suka kara tabka kuskure aka sake daukan wasu daliban. 


Ya kuma bayyana hakan a matsayin nuna rashin kwarewar aiki tare da rashin tattara bayanai don kiyaye faruwar hari na gaba, ya kara da cewa kowane lokaci matsala a bazata take zuwa musu.

Comments