Min menu

Pages

An rage kayan aure a garin Gumel Jihar Jigawa domin saukakawa samari sannan an soke lefe

 An rage kayan aure a garin Gumel Jihar Jigawa domin saukakawa samari sannan an soke lefeA wani tsari na taimako ko kuma ince tallafawa matasa masu shirin yin aure, karamar hukumar Gumel dake jihar Jigawa sun sanar da rage abubuwa masu yawa na game da aure domin a bewa masu son yin auren na daga samari damar shigewa daga ciki.

Wanda hakan da akai ba karamin taimakawa zaiyi ga duk wani wanda keda burin yin aure musamman samari masu burin yin aure kuma basu da dama saboda kudaden da ake kashewa wanda su kuma basu dashi.


Cikin abubuwan da za a rage harda LEFE wanda shi kusan sokeshi ma akayi,kuma koda ba soke shi akai ba kayan da ake bukatar a saya ba a yarda ya haura na dubu dari ba kadai.

Ga jerin abubuwan da aka rage ko aka hana gaba daya.


√ Sadaki :- Anyi gargadi ko jan kunne game da Sadaki, domin ance karda a bayar dashi fiye da kima a takaice ma dai iya yadda musulunci ya tanadar.


√ Kayan an gani ana so:- Shima wani kaya ne ko kudi da ango ke bayarwa ga amarya, wanda shima al'ada ce tazo dasu kuma suna ciwa samari tuwo a kwarya, wannan shine yasa karamar hukumar ta Gumel gaba daya tace ta soke shi, dan haka babu kayan an gani ana so.


√ An hana shagulgula da yawa irinsu kauyawa day, fulani day, dadai sauransu.


√ Sannan an hana duk wasu kade kade da zai cakuda maza da mata.


√  Kayan saka rana ma an hana kuma akwai horo ga duk wanda ya taka doka


√ Zuwa daukar amarya ma da motoci uku kawai aka amince karsu haura haka.


√ Koda za ayi kayan lefe to kayan sawa guda shida aka amince dasu sai takalmi da dan kunne da sarka sai dan kayan kwalliya kala biyu, kar a kara daga kansu.


Hakika wannan dama ce damu samari muke nema tun dadewa wannan shine zai bamu damar yin auren mu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, kuma shine zai baiwa wanda suke da mata daya damar su kara ta biyu masu biyu suyi ta uku ba tare da damuwar komai ba.


Hakika wannan hukuncin yayi daidai Allah yasa ko ina su amince suma suna irin wannan

Comments