Min menu

Pages

Ta kashe abokinta saboda karya tona asirin cin amanar mijinta da take

 Ta kashe abokinta domin boye sirrin cin amanar mijinta da take yiRahotanni sun bayyana cewa an sami labarin wata mata  a lagos bisa zargin kashe abokinta bayan ya kamata da laifin cin amanar mijinta a bayan fage, matar wanda aka kira da suna Esther Irawo. 

Rahotanni sun bayyana cewa matar ance abokinta ya  kamata dumu –dumu tana cin amanar mijinta.

Matar mai shekara 38 wanda uwace ga ‘ya’yaye biyu an zargeta da kashe abokinta har lahira mai suna Femi,  Matar ta kashe Femi bayan tayi zarginsa da kokarin tarwatsa rayuwar aurenta a kokarinsa na fadawa mijinta ya kamata dumu-dumu tana  rayuwar cin amana da wani mutum,

Mahaifin marigayin Femi mai shekara 72 ya bayyana cewa yaji dansa Femi yana kururuwa da kakari a cikin dakinsa a lokacin da Irawo ta shakeshi, mahaifin marigayi femi ya kara da cewa a lokacin babu wanda ya damu da abin dake faruwa a tsakaninsu saboda karfin abotar da kowa ya sani tsakaninsa da ita.

Mahaifiyar  wanda aka kashedin mai suna  Rose Afolabi a bangarenta, tace a iya saninta Femi bai taba yin Magana ba akan mijin Irawo ba, ta kara da cewa saidai idan wani ne  dabam  yayi kokarin fadawa mijin nata.

Matar da aka zarga da kashe abokin nata domin ta samu damar  boye sirrinta na cin amanar da takeyi a bayan idon mijinta, har wayau an sake kamata da zarginta kokarin kashe tsohon mijinta mai shekara 31, mutumin  mai suna Ezra Joseph Irawo tayi kokarin halakashi ta hanyar saka masa guba a abinci. An gano cewa bayan yaki cin abincin ta tayar da hankali tare da hayaniya daga bisani kuma ta zubar da abincin sannan ta ajiye masa dansa tayi ficewarta daga gidansa.

Mijin nata wanda ya tabbatar da matar tasa tana cin amanarsa yace Irawo ta zata Femi ne yayi masa bayanin neman mazan da takeyi a bayan idonsa. Dadi da kari kamar yadda ya bayyana yace a dan baya-bayannan ya sani da kansa, sannan mutanen dake yankin suma dayawa sun fada masa komai.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sanda na jihar Lagos DSP Elkana Bala, ya tabbatarwa da manema labarai da faruwar wannan al’amari, ya kara da cewa suna bin sawun  Irawo domin su kama bayan ta tsere. “mu samu bayanin wata mata wanda akace mana tayi hayar yan daba domin su kashe dan mutumin daya riketa, Femi Afolabi, ta fadawa mijinta taganta da wani mutum a hotel”

Matar da ake zargin har yanzu ba’a sameta ba tun a wannan ranar da abin ya faru ta gudu. Yan sanda sunce har yanzu suna bincike domin gano inda matar take, Elkana Bala ya fada”

Comments