Min menu

Pages

Ka sauka ko ka kawo karshen wannan ta'addancin an Gargadi shugaba Buhari

An kira Buhari akan ya sauka in bazai iya kawo karshen matsalar ta'addanci baMatsalar ta'addanci dai itace babbar abinda ke damun kasar Nijeriya a yanzu musamman yankin arewa.


Wani hadimin Gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje mai suna salihu yakasai yace yayi kira ga gwamnatin Nigeria cewa ta kawo karshen ta'addancin da akeyi kota sauka.


Salihu yakasai yayi wannan kirane a daidai lokacin da yan ta'adda suka sake garkuwa da dalibai da yawansu akalla yakai dari biyu a makarantar yan mata na jangebe dake a jihar zamfara. Yakasai yace wannan abin kunya ne ga Gwamnatin APC na Gaza baiwa rayuka da dukiyoyin al'umma kariya.


 Yakasai ya kara da cewa idan har gwamnati bazata iya shawo kan wannan al'amari ba to ya kamata tayi murabus.

Salihu yakasai ya wallafa wannan ne a yayin yake martani dangane da labarin sace daliban makarantar jangebe da aka wayi gari dashi.

A yau juma'a ne dai aka tashi da sabon tashin hankali a jangebe dake jihar zamfara dangane da sace dalibai da wasu yan bindiga sukayi.

Wannan dai na zaman  daya daga cikin manyan garkuwa da mutane hudu da akayi arewa maso yammacin Najeriya da akayi, wannan al'amari dai ya zama tamkar wani wasan kwaikwayo ta yadda ake sace daliban kuma bayan an dawo dasu a kwashi wasu.

Dangane da wannan ko wane mataki gwamnatin Najeriya zata dauka?

Comments