Min menu

Pages


 INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN


Sun Kashe Shi Saboda Naira 3,500


Sharifuddeen Sale Kanya da yake matakin karshe (400L) a jami'ar kimiya ta jihar Kebbi dake Aliero ya gamu da ajalinsa, inda wasu suka kashe shi jiya bayan cinikin wayar selula.


Rahotanni sun nuna cewa bayan ya tura musu kudi 3500, suka ba shi wayar, bayan ya koma makaranta ne ya ga banki sun dawo masa da kudin, sai ya koma don ya ba su kudinsu, shine suka rufe shi da duka suna ihu barawo, suka yi masa dukan kawo wuka, ya samu karaya biyar da munanan raunuka.


Daga baya aka garzaya da shi asibiti amma daga karshe ya amsa kiran Ubangiji Mahalicci.


Rahotanni sun nuna cewa a dazu daliban jami'ar sun gudanar da zanga-zanga, inda ya kai ga rufe makarantar har illamasha Allah. 


Daga karshe muna neman gwamnati ta dauki kwararan mataki don ganin an hukunta duk wanda keda hannu a faruwar lamarin.

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments