Min menu

Pages

Matashi Ya Kashe Kansa Bayan Da Budurwar Sa Ta Yaudare Shi


 TIRKASHI| Matashi Ya Kashe Kansa Bayan Da Budurwar Sa Ta Yaudare Shi 


Wannan matashi dalibi ne a jami'ar gwamnatin tarayya dake jahar Jigawa ya kashe kansa bayan da budurwarsa ta yaudare shi.


Rahotanni sun tabbatar da cewa sun dade suna soyayya da wannan budurwa ta shi ne a wannan jami'a kafin ta yaudare shi har ya kashe kansa.


Jami'ar Tarayya da ke Dutse FUD, a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin ɗalibanta da ake zargin ya kashe kansa bayan wata taƙaddama ta shiga tsakaninsa da budurwarsa.


Ana zargin matashin ya kashe kansa ne ta hanyar shan wani abu da ake zaton guba ce bayan budurwarsa ta zarge shi da kula wata daban ba ita ba.


To sai dai jami'ar ta FUD Dutse ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike kan al'amarin.


Daya daga cikin abokan karatun mamacin ya shaida wa BBC cewa al'amarin ya faru ne a unguwar Yalwawa inda marigayin da budurwar tasa da sauran ɗalibai ke haya, bayan ya koma gida daga makaranta

Haka zalika abokin nasa ya ce matashin ya kashe kansa ne bayan da budurwar tasa da ke aji biyu a sashen tattalin arziki wato Economics, ta ce ta daina soyayya da shi a lokacin da suka je wani wurin cin abinci, a ranar masoya ta duniya a Lahadin da ta gabata, sakamakon ganowa da ta yi cewar yana kula wata bayan ita.


"A ranar Valentine Day ne shi saurayin ya ɗauki budurwar tasa suka je kantin Sahad Store a Dutse. Bayan nan ne sai ita budurwa tasa ta ji labarin cewa ya je ya kula wata ba ita, wannan ne ya jawo hargitis da hatsaniya har suka rashin jituwar da ta ce ta haƙura da shi.


"Wannan taƙaicin rabuwa da shi da ta ce ta yi ne ake tunanin shi Abdul ya sa ya sha wani abu da ya kawo ƙarshen rayuwarsa.


"A ranar Litinin ma ya shiga lakca, bayan nan ne kawai sai aka ji an kwantar da shi a Asibitin Koyarwa na Jami'ar, daga nan kuma sai ya rasu," a cewar abokin mamacin.


Jami'in hulda da jama'a na jami'ar FUD Abdullahi Yahya Bello ya ce, har yanzu suna ci gaba da gudanar da bincike kan al'amarin, sannan suna ci gaba da tantance bayanan don gano ainihin abun da ya kai ga mutuwar ɗalibin nasu.


"Tabbas wannan abin yafru jiya Litinin amma muna kan bicnike. To da farko dai abin da ya fara yawo a shafukan sada zumunta ne shi ne an ce yarinyar ce ta yaudare shi, to amma daga baya ita ma ta wallafa saƙo cewa shi ne ya yaudare ta.


"A yanzu dai idan ba bincike ne ya kammala ba ba za a iya sanin taƙamaimai abin da ya faru ba," a cewar Abdullahi Bello.


BBC ta tuntuɓi rundunar ƴan sandan jihar Jigawa amma ta ce lamarin bai zo gabanta ba, da zarar ya zo za ta magantu.


Tuni dai aka binne mamacin kuma ana zaman makoki a gidansu da ke Unguwa Uku a Kano.


Wannan batu dai ya ja hankulan al'umma a ciki da wajen makarantar musamman ma ɗalibai, da kafafen sada zumanta.


A watannin baya ma wani matashi ya kashe kansa a Kano sakamakon aurar da budurwarsa da iyayensa suka yi ga wani daban ba shi ba.


Faruwar irin wannan al'amari baƙo ne a kasashen Hausa, sai dai masu sharhi kan tarbiyya na alaƙanta hakan da yawan kalle-kallen fina-finan ƙetare da suka jiɓinci soyayya


Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments