Min menu

Pages

An jefar jaririya sabuwar haihuwa an gudu amma an bar Rubutacciyar wasika

 An jefar jaririya sabuwar haihuwa an gudu amma an bar Rubutacciyar wasikaHakika yanzu mun shiga wani zamani mai wuyar sha'ani wanda aikata abu maras kyau ya zama ruwan dare, ta kowanne bangare aikata kuskure muke yi yaya baza muna haduwa da jarabawowi kala kala ba?

Wannan jaririyar da kuke gani wata ce ta jefar da ita, ta sakata a cikin kwali ta jefar da ita sannan ta rubuta wata takarda mai kama da wasika ta ajiye su tare da jaririyar. Cikin wasikar tata ta nuna cewa wannan cikin da tayi ba a son ranta bane ta hadu ne da wani ya yaudareta yace zai aure ta harta amince dashi suka aikata wannan alfashar, bayan sun aikata kuma ya gudu ya barta bata sake jin duriyarsa ba.

Wasikar tana kasan rubutun in kun duba acan kasa

Bayan ta nuna hakan sai kuma tace sunan jaririyar data saka mata shine barira.

Ta kara da cewa zata tafi ne ta barta bada son ranta ba.

Ta kuma yiwa jaririyar tata addu'a cewar Allah ya raya ta ya sa ta fada hannu na gari.

Hakika ya kamata a tashi tsaye mata ya kamata kuna hankali da duk wani da yazo yace yana sonku zai aure ku ku daina yarda da duk wanda yace ku bashi kanku da nufin zai aure ku, domin mafiya yawan samari daga zarar sunyi amfani daku sun gudu shikenan wasu ma baza ku sake ganinsu ba sun tafi kenan.

Dan haka kuna duba kamilin mutum ba wanda zai rudeku da zance ko dadin baki ba.

Haka kuma samari kuna yin adalci tsakanin ku da yan mata ku sani yaudara babu kyau kuma duk yarinyar da kuka yaudara sai Allah ya saka mata.

Domin kuma zaku haihu kuma koda baku haihu ba za a rama akan kanne da yan uwanki.

Daga karshe muke addu'a duk masu hali irinna wannan dama sauran su Allah ya shirye su.


Ko kwanan baya an samu irin wata ma ta jefar da jaririnta ta gudu ta barshi bata san hannun da zai fada ba.


Comments