Min menu

Pages

Yadda zaki kamo zuciyar saurayinda kike so koda ba garinku daya ba

Yadda zaki kamo zuciyar saurayinda kike so koda ba garinku daya baYar'uwa shin kin taba shiga wani hali na kamuwa da kaunar wani wanda ba garinku daya ba, kuma hakan ma baisan kina sonsa ba?

Shin kina ji a ranki idan ya gane hakan zai soki ko kuma ince zai amince dake?

Yar'uwa kafin na kaiki da nisa bari na fada miki ki sani shi garin masoyi baya nisa inji masu iya magana domin a duk lokacinda tsuntsun sonki ya dira a bishiyar so na wani har yayi gida to zaiyi kwai kuma ya kinkishe, saidai ki sani alhakin hakan ya rataya ne a wuyanki.

Saboda haka, yar'uwa ina fatan kin fahimci abinda nake nufi anan, domin daga zarar kin kamu da son wani to tsuntsun sonki ya sauka akan bishiyar sonsa, dan haka ki sani bayan yayi kwai zaice zaiyi kinkisar kwan dan haka sai kin dage kinyi kokari tukun zaiyi wannan kinkisar.

Yar'uwa domin wasu yan matan malalata ne, domin ko so zai kashe su baza suyi wani kokari ko hobbasa ba dan haka ke dole sai kin tsaya matuka domin ki tabbatar da kinyi nasar a soyayyarki.

A baya nayi magana ne akan yadda budurwa zata sa saurayi ya kamu da sonta to saidai wancan bayanin yana nuni ne da cewa in suna gari daya ne, dan haka yanzu naga ya dace na fada muku hanyar da zaku bi saurayi ya kamu da sonku koda ba garinku daya ba.

A lokuta da dama lamarin soyayya abu ne mai wuyar sha'ani yakan saba da mahimtar mutane daban daban, saboda haka anan zan kawo muku yar fahimta ta daidai gwargwado.

Kafin naje da nisa yar'uwa shin kinsan cewa idan bakwa tare da saurayi ma'ana ba garinku daya ba dole sai kinyi amfani da hanyoyin sadarwa kamar waya, rubutun wasika ko kuma sakon baki.

Kafin nayi nisa bari nayi wasu yan tambayi

1 shin da akwai sanayya a tsakanin ku?

2 shin ya sanki fuska da fuska?

Kafin na kaiki da nisa yar'uwa, tsakanin masoya duk wanda ya fara kamuwa da so to gaskiya yanada aiki a gabansa dan haka dole kiyi duba da..

* Halayensa

* Dabi'unsa

* Alakarku dashi kafin ki fara sonsa

* Salonsa gun jan aji


1 :- Halaye

Yar'uwa gane halayen mutum kamar samun kansa ne domin duk wata hanya da zata saki rudani akan sa indai kika san halayensa kin gama sanin lagonsa, dan haka kafin ki tunkareahi yanada kyau ace kin san halayensa koda kadan ne.


2 :- Dabi'unsa

Nan ma idan kika karance shi da dabi'unsa kin wuce wani guri mai wahala dan haka in har kin kamu da son saurayi kafin ki tunkareshi yanada kyau kisan wacce dabi'a gareshi.

3 :- Alakarku dashi

Anan zai iya kasancewa dan uwanki ne a wani gari, kuma zai iya iyuwa ta social network kuka hadu ko kuma wani ne ya hadaki dashi, to anan kafin ki tunkareshi yanada kyau ace kin shirya amsa tambayoyi kamar haka

- Wace ce?

- Ina kika samu numberta?

- Ina kika sanni?

4 Salonsa gun jan aji

Wannan zai iya zama halayyarsa saidai kuma zai iya kasancewa wasu yan mata kawai yake yiwa dan haka kada kema kiyi mamaki dan ya ja miki aji. To anan salonsa zaki gane wajen jan ajin ke sai kiyi kasa da naki ajin tunda kece kika fara sonsa.

√ Hanyoyin sadarwa tsakaninki dashi

hanyoyin sadarwa tsakanin ke dashi anan sun hadar da.

- Lambar waya

- WhatsApp

- Facebook

-  Telegram

-  Sakon baki

- Rubutacciyar wasika

Kafin ki fara amfani da wadannan hanyoyin dole ki kintsa domin sai kin juri

• Yawan gaisuwa

• Iya magana ko furuci

• Iya daukar photo

• Iya bada labari

Gaisuwa

A online ko ta message zai saka saurayi ya bibiya mai tura masa wannan sakon kuma zaina jin dadi dan haka kema saikin juri haka kuda bakya ganin reply.

Iya gaisuwa

Anan duk lokacinda gaisuwarki ta fara amfani saiki juri iya lafazi da kalamai masu dadi da zaisa saurayinda kike so zai tsaya sauraronki.

Iya daukar photo

Nan ma suna aiki ne idan ta kama kamar a WhatsApp ko facebook zaki iya daukar photonsa ki hada da naki ko kuma ki dora nasa kadai sannan kiyi kalamai masu dadi a kasa koda kuwa yabonsa ne wannan zai taka rawa sosai.

Idan kuma naki photunan ne sai ki rika dora masu kyau sosai.

Iya bada labari

Yana da kyau kisan irin labarin da yake so dan haka idan har kin gane shi zakina yawan bashi, wannan yana sa saurayi yaji kinyi masa kuma kina birgeshi.

Alamomin da zasu nuna ya kamu da sonku

Sun hadar da kiranki a waya kafin ki kirashi

Yi miki magana ko bakya online

Liking da duba status naki

Yawan tambayar lafiyarki

To daga wannan lokacin shikenan kin gama komai domin a zuciyarsa ya fara sonki.


Comments