Min menu

Pages

 Ci gaban labarin


Banyi masa musuba na mika masa dan makullin motar na koma gefe na tsaya ina kallonsa ya tada motar sannan ya bata wuta lokaci guda yasa mata giya ya fisgeta baiko dubi inda nakeba ballantana har yaga hannun da nake ta famar daga masa.

Innan a tsaye har saida na daina hango danjar motar tasa sannan na shiga gida, kasancewar dakina a bakin kofa yake sai kawai na shiga ban tsaya bata lokaci ba na cire sabin kayan nawa na ajiye a gefe guda dan kar karin gugar nasu ya baci dan kuwa dasu nake sa ran komawa gun husna gobe.

Bayan na saka tsofin kayana sai kawai nai tsalle na hau kan tsohuwar katifata kura ta turnike kamar ana sukuwar dawakai nanfa gadon bayana ya sage saboda buguwar da nayi a jikin busheshshiyar katifar tawa bansan lokacin da nayi kara gamida mikewa tsayeba.

Na dade a tsaye bayana a sankare kamar wanda aka dakeni da sanda sannan na samu bayan nawa yadan dawo saiti.

Na dan karasa inda katifar take na hau cikin sanda dan gudun abinda taimin dazu na jingina da bango ina tunani da nazarin yadda soyayyata zata kasance da husna a haka har bacci ya zagayo ya daukeni..

Zafin ranar gamida haskenta suka doki fuskata nai sauri na tashi daga nannauyan baccin da nake naga ashema gari ya waye har rana ta fito, abin yayi matukar bani mamaki saboda wannan makarar da nayi dan kuwa ni iya sanina nasan na kai shekara uku ban makara irin yauba..

Nai sauri na mike daga kwancen da nake sannan naje nai alwala nai sallah...

Bayan la'asar tayi munyi sallah naje nai wanka na shirya tsaf nasa kayana sannan na kama hanyar zuwa gidansu gimbiyata husna.

Na dade ina tafiya da kafafuna sannan na samu na karasa kofar gidan ai kuwa tun kafin na tsaya naga itama ta fito kamar tasan cewa na iso.

Da tattausan murmushinta ta tareni sannan taimin umarni damu karasa cikin gidan nasu..

Banyi mata musuba ta shige gaba na bita a baya har muka karasa cikin farfajiyar gidan, cikin gidan an kawatashi da kayayyaki na alatu da jin dadin rayuwa ga shuke shuke masu matukar kyau da daukar hankali furenninsu sai kamshi suke.

Karkashin wata bishiyar zaitun nan ne inda husna ta tanada mana ma'ana nanne inda za muyi shirar da ita a wannan yammacin...

Bayan ta nunamin wata kujerar roba da take girke a gun su biyu suna fuskantar juna sai kuma dan wani tebir da aka ajiye a tsakiyar kujerun ma'ana sune suka raba tsakanin kujerun...


Ban jira komaiba na karasa na zauna itama tazo ta zauna a daya kujerar muka fuskanci juna nida ita babu wanda yace da wani kala, saida muka dauki lokaci muna kallon kallo nida ita sannan husnan ta katse shirun namu da murmushinta mai daukar hankali sannan ta fara yimin magana da yar siririyar muryarta mai kamar ana busa sarewa tace dani...


Yaya Abdul ashe dama zaka zo?


Murmushi kawai nayi sannan na dubeta har cikin idanunta nace haba husna menene zai hanani zuwa gareki in har ina raye?


Gaskiya naji dadin zuwanka sosai dan wallahi jiya kusan kasa bacci nayi saboda kewa da kuma tunaninka harma so nake gari yai saurin wayewa na kiraka na danji muryarka sai kuma na tuna ashe baka da waya husna ta sake cewa dani tana wasa da yatsun hannunta...

Murmushi kawai nayi sannan nace karki damu husna ai gashi nazo gareki dan kuwa nima kaina saida tunaninki ya dinga kaiwa da komowa a cikin zuciya naji babu wacce nake kaunar sake gani kamar ke kunnuwana kuma muryarki kawai suke bukatar suji nima nai mata wannan furucin...

Na gode kwarai yaya Abdul dina gashi kuma mun tsaya sai zuba muke ko ruwan sha ban kawo maka ba na barka da yunwa gamida kishirwa husna ta fada tana kokarin mikewa tsaye daga kan kujerar da take...

Husna kenan aini babu wata yunwar da nakeji a halin yanzu tunda ina tare dake haka kuma zan iya shafe tsawon wasu kwanaki ba tare da naci ko kuma nasha wani abuba idan har kina kusana dan kuwa sautin muryarki shi kadai yakan gusarmin da yunwar da nakeji haka kuma ganin wannan kyakkyawar fuskar taki mai annuri yakan kawarmin da kishirwar da nakeji nace da ita...

Lumshe idanunta kawai tayi sannan ta bude ta dubeni tace yaya abdul kalamanka suna matukar birgeni ina jin dadinsu sosai da sosai dan haka jirani ina zuwa tana maganar ta kada kanta ta nufi cikin gidan nasu..

Nai shiru ina tunanin wannan hali na mutuncin da husna taimin na dubi girman gidan gamida tsarin da yake dashi na kuma tuna yadda tsarin namu gidan yake na kasa ne haka kuma ya tsufa dan kujejjen rufinsa duk yayi baki saboda yawan shekarunda ya shafe, muna matukar shan wahala musamman idan lokacin damuna ne dan kuwa idan har ana ruwa to kusan a tsaye muke kwana saboda fashewar da rufin dakunan gidan namu ke dashi na girgiza kai na tuno cewa wai idan zanyi aure dole sai dai a bani daya daga cikin tsofin dakunan dake cikin gidan na tare da amaryar tawa...

Anya kuwa husna zata amince ita da take zaune a cikin wannan katafaren gidan?

Na tambayi kaina lokaci guda ina tunanin girman matsayinta.

Mezai hana ta amince idan har tana kaunar taka wata zuciyar ta fadamin...

Gaskiya akwai abin mamaki idan har husna zata iya zama a gidanmu dan kuwa ko kusa baiyi tsari da irin gidajen da yayan manyan masu kudi suke zaman aure a cikiba sauda dama nakanga babu wani da yake auren yar gidan mai kudi sai yayan masu kudi ko kuma yayan sarakuna da kuma manyan yan siyasa..

Haka kuma sau tari yayan talakawa sunfi auran ruwansu ma'ana yan uwansu talakawa..

Ban gama tunaninda nakeba sanadin zazzakar muryar husna da takemin magana..

Firgigit nai saurin daga kaina na dubeta sannan wani dan fatalwan murmushi ya subuce daga fatar bakina...

Yaya Abdul dina tunanin me kake haka? Husna ta tambayeni tana kallona...

Tunani kuma husna? Na maida mata da tambayar da tayi a gareni...

Eh tunani mana abdul, dan Allah tunanin me kake? Ta sake tambayata.

Husna tunanin yadda rayuwarmu zata kasance gaba nakeyi  musamman idan na tuna yadda zamu rabu dake nai mata karya a karo na farko, wanda ni kaina nasan ta gane hakan.

Kuramin ido tayi kamar wacce zata gano abinda ke damuna sai kuma lokaci guda tayi murmushi ta zauna a kujerar da ta tashi dazu.

Ta dade idanunta suna kaina ni kuma na kasa cewa kala tun daga maganar da na fada mata tun dazu, yaya Abdul waye ya fada maka zamu rabu haka kuma wa zai rabamu da kai? Lokaci guda ta jeromin wadannan tambayoyin nata har guda biyu...

Husna a hakikanin gaskiya ke baki kasance daga cikin irin matannan da suka taso cikin wahala da talauciba haka kuma ina tunanin rana a tsaka bazaki iya samun kanki a cikin irin wannan halin ki jure ba na sake cewa da ita..

Eh abdul maganar da ka fada ta farko gaskiya ne cewar na taso cikin jin dadi to amma waye ya fada maka bazan iya jure zaman talauci ba? Husna ta sake tambayata...

A gaskiya husna ina tunanin bazaki iya zama a gidan mu ba dan kuwa gaskiya a yadda naga gidanku yadda kika taso cikin jin dadi bani tunanin zaki iya zama a gidanmu mu talakawa..

Karka damu abdul in dai nice bana tunanin akwai yanayin da bazan iya jurewa ba indai akanka ne dan haka rike wannan ta mikomin wani abu a cikin leda..

Nai sauri na dubeta nace husna menene a ciki haka da kikamin kyautarsa?

Waya na saya maka abdul dan kawai muke magana dakai idan bama tare dan na dinga jin daddadar muryar nan taka haka kuma naji a wanne hali kake ciki dan wallahi ko kusa banso kayi nesa dani, dan sai naji kamar wani abune zai sameka idan bama tare ko kuma  watace zatamin kwacenka hakan tasa dazu da rana naje na sayo maka ita husna ta sake cewa dani...

Hannuna yana rawa na karba lokaci guda na bude kwalin wata hadaddiyar waya na gani irin wacce ake yayi irin wadda duk wani maiji da kansa zaiso ace irin wayar yake rikewa tun daga kan manyan samari har zuwa manyan yan mata haka kuma yayan manyan masu kudi ko kuma masu mulki...

Na bude baki da niyyar nayi godiya a gareta amma tun kafin nace komai tai saurin rufemin bakina da hannunta sannan tace haba yaya abdul ai bai dace kamin godiya ba danna sayama waya kuma naga idan banyiwa masoyina abin kaunata abuba wa kuma zanyima dan haka kome nayi a gareka ko kadan bana bukatar sai kamin godiya husna tace dani...

Shiru nayi ina kallonta harta gama maganar da takemin sannan nayi murmushi nace husna kenan, ai ya zame dole a gareni nayi godiya sakamakon irin kaunar da kike nunawa a gareni wanda hakan yakesa ni kuma zuciyata take kasa nutsuwa idan harba godiyarnan nayi a garekiba domin husna...na kasa karasa maganar saboda tsananin dadin da yake kai kawo a cikin zuciyata...

To abdul nima na gode husna tace dani tana kallon can wani bangare mai tarin shuke shuke dake cikin gidan...

To husna nikam zan wuce dan haka sai goben idan na dawo ko kuma idan munyi waya dake dan haka bari na fada miki number tawa saiki ajiye dan kuwa dama na fada miki inada layi wanda nake amfani dashi da kafin bukata ta tasomin na sayar da wayar...

To yaya abdul fadamin number husna tace dani lokacinda ta zaro tata wayar abin yayi matukar birgeni dan kuwa itama tata wayar iri daya ce da wacce ta sayamin..

Uhm nai murmushi sannan na fara da bata number tawa kamar haka 08060763027...

To shikenan zan kiraka da an jima dan haka karbi wannan kasa kati danka kira sauran yan uwa da kuma abokanka husna ta fada lokacinda ta mikomin daurin kudi yan dubu dubu...

Ji nayi gabana ya fadi kirjina ya buga da karfi lokacin da naga wannan daurin kudin dan kuwa nidai tunda nake ban taba kawo cewa zan mallaki kudin da zai kai yawan wadannan ba har zuwa lokaci mai tsawo na dubeta sannan na dubi kudin dake hannunta na girgiza kai nace haba haba husna gaskiya bazan karbi wadannan kudaden nakiba dan kuwa idan har maganar gaskiya za ayi to nine ya dace ace na baki bawai kece zaki baniba...

Wani lokacin kana bani mamaki yaya abdul da har kake wani mamaki idan nayi maka abu na sani idan kaima kana da halin yin hakan ai zakamin abinda yafi wannan ma dan haka ka karba idan harba so kake ka batamin raina ba husna ta fada wannan karon kam bata rai tayi tana kallona...

Nai saurin karbar kudin sannan nace husna na karba dan haka daina bata rai dan kuwa ko kadan banso naga kin damu...

Murmushi kawai tayi sannan tace yauwa abdul dina har kasa naji dadi a cikin raina...

To shikenan husna nizan wuce saina jiki idan munyi waya nace da ita...

To yayana husna ta fada lokacin da ta takemin baya ta rakoni har kofar da zata fitar dani daga cikin gidan nasu sannan mukayi bankwana da ita na kama hanyar da zata kaini gida zuciyata cike da murna gamida farin cikin abinda husna tamin da haka harna karasa kofar gidanmu..

Ina zuwa na fita da gudu na shiga zauren gidanmu idanuna a rufe saboda murna karon da naji nayi da mutum ne yasa nai saurin bude idanuna mubarak na gani a tsaye nai saurin dubansa nai dariya sannan nace wallahi kado ta sayamin waya mai matukar kyau...

Waye ta saya maka wayar ne da zaka zo har kana hankadeni...

Wa kake tunanin zata sayamin waya idan ba sarauniyar mataba? Ai kaima kasan wannan aikin sai tauraruwar taurari mai hankali tarbiya tunani gamida sanin daraja da girman mutane mai yawan taimako...

Abdul kenan, ni sai fadamin halayen mace kakeyi kuma kaki fadamin sunanta ai yana da kyau ka fadamin sunanta danna gane mubarak ya sake fada...

Husna mana ai kaima kasan itace zatamin irin wannan kyautar na fada ina kallonsa...

Ban jira ya sakemin magana ba kawai na wuce cikin gida..

Haka mukaci gaba da soyayya da husna har tsawon wata biyar ya zamana kowa a gidansu yasanni haka nima kowa ya santa a gidanmu hakan kuwa ya biyo bayan gwagwarmayar da husna tasha akan sai an barta munyi aure saboda jajircewar da sauran yan gidansu sukayi akan bazata auri talaka irina ba daga karshe sai kuma komai ya zama tarishi ya zamana sun amince akan ta aureni...

Munyi matukar farin ciki lokacin da aka yanke ranar aurena da husna abbanta ya bamu wani hadadden gida wanda zamu zauna nida gimbiyata husna...

Haka mukaci gaba da zama cikin farin ciki har ranar daurin aurena da husna tazo..

Ba laifi ansha biki sosai da sosai an cashe duk kan abokaina sun ziyarci auren nawa tun daga kan maza har zuwa mata...

Bayan dare yayi abokaina su sadauki da mubarak da sauran abokaina guda uku sukamin rakiya zuwa dakin bayan yan sauran maganganun da abokaina sukayi mana nida gimbiyar tawa amatsayin nasiha sai kuma sukacemin zasu tafi...

To shikenan bari nayi muku rakiya koda bakin kofane nace dasu...

Haba yaya abdul ai ba'a raka abokai tunda kaima kaga rakoka sukayi dan haka ka barsu su tafi amarya husna tace...

To amarsu ta ango mu yau saiya rakamu waje tukunna ko an fada miki guduwa za muyi dashine sadauki ya fada yana dariya...

Karki damu gimbiyata yanzu zan dawo nace da ita lokacin da na takewa abokan nawa baya mukayi waje...

To yaya abdul a dawo lafiya husna tace dani..

Tunda na rakasu bakin kofar mukai bankwana dasu sai kawai na nufo ciki dakin da amaryata take cikin farin ciki da zuwan wannan daren mai suna DAREN FARKO...

Kaina ne ya sara da karfi lokacinda na shiga cikin dakin numfashina ya fara sarkewa idanuna ya fara lumshewa wani jiri ya fara daukata naji na tafi luu zan fadi nai sauri na dafa bangon dakin da hannuna sakamakon ganinta da nayi a kasa mala mala cikin jini...


Akwai ci gaban labarin

Comments