Min menu

Pages

Salma labarin fatalwa

 


Farkon labarin Mai kyauce ta gani ta fada farace mai madaidaiciyar fiska gashin kanta bakine dauke take da idanu masu matukar kyau da daukar hankali sanye take da fararen kaya masu matukar fari kanta dauke take da wani kambu irinna yayan sarakuna hannunta rike da wata sanda mai kyau dauke da zane irinna sarauta sai sheki take tana tafe akan iska ma'ana ita ba a kasaba ita kuma ba'a sama ba... Ta dubeni ta haskakeni da wani murmushi sannan tace dani kayi haquri masoyina abdul ina kaunarka a rayuwata ina sonka a ruhina zuciyata tana begenka ina yawan tunaninka abin sona bana tunanin zan iya hakuri dakai duk rintsi da tsanani kai nake tunani, sannu a hankali ta fara saukowa kasa tazo har kusa dani sannan ta kama hannuna ta ciri wani zobe mai matukar kyau dake hannunta ta samin sannan tace karka manta dani masoyina abdul abin alfaharina a duniya dama garinda nake a yanzu.. Lokaci guda naga kayan dake jikinta sun fara sauya kala daga kalar farare zuwa ja sannan gashin kantama naga ya tarwatse ta dubeni tace Ko kadan karka bewa kowa zobena domin aikata hakan a gareka kuskurene mafi muni.. lokaci guda sainaga ta bace kuma a lokacin na tashi daga barcinda nake sai a lokacin na gane ashe mafarki nayi to amma abin mamaki lokacinda nakai dubana hannuna sai naga zobenda ta samin mai matukar kyau ajikin zoben anyi rubutu da kyawawan harufa an rubuta marigayiya SALMA abin yayi matukar tsorata ni kuma ya dimautani yayama za ayi nayi mafarkin abin sannan daga baya kuma na ganshi a baiyane, to wayece kuma marigayiya SALMA na tambayi kaina idan har kuwa marigayiya ce tome take nufi dani dan kuwa ni a iya sanina duk wanda aka cewa marigayi ko marigayiya to ana nufin sun riga sun mutune dan haka yanzu matar da nayi mafarki da ita ta mutu kenan kuma shine har take cemin masoyinta kuma abin kaunarta ko dama ana soyayya da mutanen da suka mutune na kuma tambayar kaina? Idan har kuwa ba'a soyayya dasu to ko tantama banayi macen da tazomin a mafarkina ta yanzu FATALWA ce... Lokaci guda tunanina ya tsaya naji na sake tsorata jikina ya dau rawa cikin sauri na tashi gaba daya hankalina ya tashi na dubi zoben abin mamaki sai naga ya canja kala haka kuma sunan dake jikin zoben ma ya canja ada farko marigayiya SALMA ne a rubuce amma kuma yanzu sai naga ya koma fatalwa.

Fatalwa!! Na fada da alamar tsoro karara a fuskata, zuciyata ta fara dukan uku uku kamar ta fasa kirjina ta fito waje to wai me ake nufi da fatalwa ne na tambayi kaina lokaci guda cikina yayi wani kugi saboda tsorata hannuna na rawa nai sauri na kama zoben da niyyar cirewa abinda na gani shine yafi komai firgitani domin rubutun dake jikin zoben ne ya sake sauyawa haka zalika kalar zoben ma ta sauya launinsa ya koma kamar launin jini sunan dake jikin zoben ya tashi daga fatalwa zuwa gargadi mafi muni wanda aka rubuta kamar haka

ko kadan karka kuskura kace zaka cire zoben a hannunka domin aikata hakan zai zamto kuskure babba a tare dakai dan haka nake umartarka daka kyale zoben a hannunka...

Nai turus na tsaya daga yunkurin da nake na cire zoben jikina sai rawa yake na rasa inda yakemin dadi.

Kararda naji wayata nayi shine yai sanadin farfadowata daga suman zaunen da nayi abin yayi matukar tayarminda hankali domin kuwa ni nasan wayar tawa a kashe take tun jiya dan haka towa ya kunna min wayar tawa kuma nidai a iya sanina wayar tawa ma ba caji ko kadan kuma nasan babu wanda ya shigo cikin dakin nawa dan haka nai sauri na karasa inda filo na yake na daga shi na dauko wayar tawa.

Lokacinda na dauko wayar daga gefen katifata na duba abinda na gani saida yasa na kusa yin ihu domin sunanda na gani a rubece kwata kwata banida irinsa a cikin wayar tawa domin ni ko mai harafin sunanma bani amma kuma sai gashi naga an rubuta Salma is calling.

Waiyo Allah na! Na fada a hankali idanuna a zare saboda tsananin tsoratad da nayi cikin sauri na danna gunda ake amfani dashi domin a katsarda kira amma abin mamaki sai naga wayar taki ta katse nai sauri na bude murfin batir din na cireshi daga ciki ko hakan zaisa ta mutu amma shiru babu abinda ya canja.

Na daga wayar da duk kan karfina na bugata da jikin bangon dakin ta fado ta tarwatse a kasa amma duk da haka karar take bata katseba hakan yasani tilas na daga wayar na kara a kunnena abinda naji tana fada shine yasa hanjin cikina murdawa da karfi naji wata hajijiya tana neman dibana kaina yayi wani dum kamar an bugamin guduma aka saboda tsabar tsoro domin cewa tayi cikin wata irin murya kamarta jaki tace yauma zanzo gareka abdul idan dare yayi dan haka ka tanadamin gunda zan kwanta kamin shimfida mai kyau masoyina.

Tana fadar hakan sai naji wayar tawa tayi shiru alamar me maganar ta daina sannan kuma sai naji wani irin zafi ya cika dakin harna zuwa wani lokaci sannan naji dakin ya dawo daidai kamar yadda yake ada na dubi kayan jikina naga gaba daya sun jike sharkaf da gumi nai shiru nadan wani lokaci ina tunanin halinda zan shiga a gaba sanadin wannan matar mai ziyarata cikin dare na tuna kalamanta na karshe a gareni da cewar zatazo yau.

Me zatazo tayi a gareni nace da kaina kuma wai har cewa take nayi mata shimfida inda zata kwanta, idan tazo me take bukatar karba daga gareni? 

Ranka takeso ta karba wata zuciyar ta bani amsa nai sauri na kawarda wannan tunanin da zuciyar tawa take saboda nasan ba alkhairi bane sai lokaci guda tunanin na sami abokina mubarak musa na fada masa halinda nake ciki ya darsu a zuciyata, to amma idan ka fadawa abokin naka kana ganin zai iya kawoma karshen matsalarta ne, ko kuma ganinka bazata iya hadawa duk ku biyun tayi muku duk abinda taga dama bane? har yanzu dai zuciyar tawa ce take dada shawartata a karo na biyu.

Kamar ance daga kanka cikin sauri na daga kaina to alokacin nai ido biyu da photonsa abinda na gani a jikin photon shine yafi komai tayarmin da hankali domin gani nayi mubarak din dake jikin photon yanamin dariya sannan naga kalarsa tana rikidewa daga kalar mubaren dana sani zuwa wata kalar.

Ada kayanda ke jikinsa wata shudiyar shaddace wadda aka mata ado amma sai naga sun koma farare tas dasu kamar likkafani sannan naga idanunsa sun zaro waje kamar zasu fado kasa suna canja kala daga farare zuwa kalar ja gaba daya fuskarsa ta zamto abar tsoro ta koma kore shar sannu a hankali harta ta dawo kamar fuskar salma.

Sannan naji magana akace dani daga jikin a photon da irin muryar da naji da farko karka kuskura ka fadawa kowa halinda kake ciki idan kuma ka fada to yanzu ranka zai zama bakon duniya kuma ya zama dan gari a lahira

Bansan lokacinda na kwala kara na fadi kasa a sumeba bude idanun da zanyi saina ganni a kwance akan gadon asibiti babana da mamana suna zaune a kusa dani sai kuma kanwata  Amira da takemin fifita na yunkura na tashi zaune akan gadon a daidai lokacinda naji su abbana suna cewa sannu da zuwa likita na daga kaina domin ganin likitan abinda na gani shine ya sani fitsari domin kuwa abin nan dana saba gani shine ya sake baiyana ma'ana SALMA lokaci guda nasa kara na kankame mahaifina ina nuna masa Salman ina cewa wallahi itace kasheni takeso tayi wayece itace tambayar da gaba dayansu sukemin na daga hannuna na nuna musu ita maganarda naji sunayi itace ta bani mamaki domin cewa sukeyi ai wannan da kake nunawa ba kowa bane likita ne hakan shine ya bani tabbacin ni kadai nake ganin abinda ke faruwa...

Nai tsalle na tsallake mahaifiyata da take zaune a bakin gadon na nufi kofar fita daga dakin da gudu hankalina ya gama tashi, nai turus na tsaya lokaci guda sanadin ganin wata salman da nayi a bakin kofar dakin kamaninta sun rikede sun juye sun koma abin tsoro...

Gashin kanta ya tarwatse ya zama wani kore kore, hakorinta sun kara tsayi kayan daga jikinta gaba daya sun rine da jini idanunta sun fito kamar zasu fado kasa

Hannunta na dama tana rike da diga irinta hakar rami daya hannun kuma tana rike da shebur na diban kasa..

Cikin sauri na juyo da baya zan koma gunsu abbana da suke tsaye suna kallona cikin mamakin faruwar wannan al'amari a gareni...

Juyawar tawa keda wuya na sake ganin salman ta rabe sun zama harsu biyar a tare kuma dukansu hannunsu diga da shebur ne a rike, cikin sauri na kuma juyawa da baya domin naje na ture wadda take tsaye a bakin kofar ina zuwa nakai hannuna gareta da niyyar tureta sai naga ta nunani da tafin hannunta abinda na gani yayi matukar rikitar dani domin gani nayi wasu farata masu matukar tsayi sun baiyana a hannunta sannan naga ta tashi sama akan iska ta nufo gareni tana zuwa ta shakeni da hannunta sannan tace dani kasheka zanyi yanzu.

Lokaci guda nasa wata kakkarfar kara nasa hannuna domin na kwace daga rukon da tamin amma na kasa koda wani motsi mai karfi ganin cewa kasheni takeso tayi hakan yasa na sake yunkurawa na fisge daga hannunta lokaci guda kuma sai naga ta bace inanan a kwance ina kallon saman dakin saboda tsananin jigatar da nayi..

Juyawar tawa keda wuya na sake ganin salman ta rabe sun zama harsu biyar a tare kuma dukansu hannunsu diga da shebur ne a rike, cikin sauri na kuma juyawa da baya domin naje na ture wadda take tsaye a bakin kofar ina zuwa nakai hannuna gareta da niyyar tureta sai naga ta nunani da tafin hannunta abinda na gani yayi matukar rikitar dani domin gani nayi wasu farata masu matukar tsayi sun baiyana a hannunta sannan naga ta tashi sama akan iska ta nufo gareni tana zuwa ta shakeni da hannunta sannan tace dani kasheka zanyi yanzu.

Lokaci guda nasa wata kakkarfar kara nasa hannuna domin na kwace daga rukon da tamin amma na kasa koda wani motsi mai karfi ganin cewa kasheni takeso tayi hakan yasa na sake yunkurawa na fisge daga hannunta lokaci guda kuma sai naga ta bace inanan a kwance ina kallon saman dakin saboda tsananin jigatar da nayi...

Da kyar na samu na yunkura na mike tsaye na juya na kalli gunda mahaifana suke abinda na gani shine abu mafi girman tsoratarwa a gareni domin gani nayi duk fuskokinsu suma ya koma irinna SALMA hatta kanwata liliane itama kamanninta sun rikede sun zama kamarna salma 

A lokacin na sake kwala wata matsanaiciyar kara na yanke jiki na fadi kasa sumamme...

Budar idanuna keda wuya na ganni a kwance a gida naga mahaifana suna zaune a kusa dani kanwata liliane tana shafamin ruwa a gefensu kuma wani malami ne a zaune yana karatu yana tofamin a jikina zubur na tashi zaune na dubi mahaifan nawa nace dasu meke faruwane a gareni?? 

A lokacinne kanwartawa liliane take cemin wai rukiyya akamin, cikin rashin fahimta na dubeta nace meya faru gareni har aka yimin rukiyya?? 

Kanwarwar tawa ta dubeni tace ai wata aljanace ta shiga jikinka wai sonka take tasha fito maka a siffar mutane tace tana sonka amma kaki ka karbi soyayyarta kace mata kai akwai wadda kakeso wato tsohuwar budurwarka data rasu a sanadin hadarin mota kuma tace itace ta shiga motar ta kunce tayar motar har tayi hatsari to shine aljanar ta shiga jikin gawar budurwar taka take maka fatalwa...

Cikin sauri na dubi kanwar tawa nace to yanzu ya akayiwa aljanar?? 

Sai kanwar tawa tace yanzu aka konata harma ta fice daga jikinka kuma tace bazata kuma dawowa garekaba..

Wannan maganarda tamin itace tasa na tuno yarinyarda tasha zuwa gareni tana cewa tana sona na kuma tuna sunanta salma itama na kuma tuna duk abinda nasha fada mata na cewa ta daina kulani..

Domin har marinta na tabayi ashe ban saniba aljanace...

Allah ya kiyaye nace a fili, su kuma suka amsa min da amin gaba daya su.

Dan haka nake dada jan hankalinmu akan mu guji wulakanta duk wanda suka nuna suna kaunarmu domin bamu san da wadanda zamu hadu dasu ba...

KARSHE. 


Comments