Min menu

Pages

Kunada labarin yanzu damfara ta koma internet? Insme sun tsere

 Kunada labarin yanzu damfara ta koma internet? ( insme sun tsere)Hakika kasuwa ko harkar samun kudi yanada kyau sosai ga mutane matasa mata da maza harma da manya da yara, saidai harkar wadda ta dace ita ce abar nema bawai ko wacce iri ba, dan haka yau nazo muku da dan karamin bayani akan wasu harkoki.

A kwanan nan na ga da yawan mutane sun mayar da hankalin su akan hanyoyin samun kudi ta yanar gizo, abin ya zama kamar wutar daji, da yawan mutane kuma ba su san abin ba kawai daga an ce ana samun kudi sai su tura kansu, wasu ba sa bincike kawai shiga suke, duk da akwai wadanda addini ya yarda da su wasu kuma kawai karya ce da damfara tsagwaronta.


Takaitaccen tarihin asalin harkar


Michael Aldrich ya mutu a shekarar 2014 shine mutum na farko da ya kirkiri online shopping a shekara 1979, daga baya kuma mutane irin su Brain Action, Larry Page, Sergey Brin, Even Spiegel's da sauransu suka kirkiri abubuwa da za ka shiga domin zuba hannun jari ko kuma ka yi kasuwanci a yanar gizo, siya ko siyarwa.


A yanzu babu wanda zai iya fada maka adadin manhajar da ake irin wannan harkallar a cikin wannan duniyar domin suna da tarin yawa, kamar irin  su chipper cash, Spin &win zeraklamy, Big Time cash, swag bucks, upwork, thredup, cardpool, gazelle, swap, offerup, your work, forex, bitcoin, coins, moth cash insme, gdax,da sauransu 


Ire-iren su


Koda take akwai na zahiri, haka kuma dole akwai  wadanda ake kirkira domin ayi damfara wanda kuma shine yafi yawa, akwai wadanda idan ka shiga kamar kanka ka fitar tsirara, wasu kuma idan ka shiga kamar ka tonawa asusunka ko ma'ajiyarka asiri ne.

Sannan akwai wadanda idan ka bude tamkar ka gayyato wa hanyoyin sadarwarka yan harkers ne, kai akwai wadanda shi kansa wanda ya kirkira bama a san shi ba, kuma yayi haka ne domin tara abin duniya ma'ana ya samu wasu yan sulalla ko kuma ince kudi a takaice, sannan kuma ya cuci mutane masu yawa.

Dan haka koda yaushe mutane su zama cikin shiri kuma suna nazari da taka tsantsan wajen shiga irin wadannan harkokin na kasuwanci, kuma mutum koda zai shiga da farko kar ya zuba kudi masu yawa idan har baisan harkar ba ko kuma harkar sabuwa ce dan haka a kiyaye

To gashi nan dai ko insme ya isa darasi a gun mutane domin sun gudu da kudin jama'a

Comments