Min menu

Pages

Ina kwanciya da maza sama da ashirin a kowacce rana inji matashiyar da akai safararta zuwa burkina faso daga Nigeria.

 Ina kwanciya da maza sama da ashirin a kowacce rana inji matashiyar da akai safararta zuwa burkina faso daga Nigeria.



Wata yarinya yar Nigeria ta bada labarin cewa tunda akai safararta zuwa Burkina faso a kullum saita kwanta da mutane masu yawa wanda akalla suka kai ashirin koma fiye da haka, matashiyar budurwar taci gaba da fada cewar duk ranar data samu sefa dubu dari, to fa bata iya gane da adadin mazan data kwanta dasu a wannan ranar.

Safarar yan mata dai wata dabi'a ce ko kuma al'ada da aka fito da ita tun waccen lokacin inda sai a dauki yan mata daga kasashen su na ainashi a fitar dasu wasu kasashen da niyyar neman kudi, to saidai mutane da dama kance neman kudin da ake fita dasu bawai wata hanya ake bi mai kyau ko ma'ana ba kawai ana kaiwa yan matan ne ana bayar dasu ga maza suyi zina dasu sannan a bada kudi.

Bawai iya kan wannan yarinyar bace ake haka kusan da yawa matan da ake daukarsu daga gurin mahaifansu a tafi dasu kasar waje da niyyar neman kudi to hakika irin wadannan guraren ake kaisu, yan kalilan ne ba wannan hanyar suke bi ba.

Dan haka muna kira ga iyayen yara dasu zuba ido sannan suyi bincike akan duk wata mata da tazo ta nuna a bata yarinya zata fitar da ita waje da niyyar neman kudi.

Sannan yanada kyau jami'an tsaro su yawaita bincike domin ganin an yiwa wadannan masu irin halin horo ko kuma a hana su fitar da duk wasu yara.

Domin wannan ba karamin abu bane na cin zarafin yan kasa.

Ko kuma asa doka mai karfi na duk wanda aka kama yana yunkurin fitar da yara ai masa girl.

Comments