Min menu

Pages

Hukuncin sakin mace cikin shirin film daga Bakin shehun malami Dahiru Bauchi

 Hukuncin sakin mace cikin shirin film daga Bakin shehun malami Dahiru BauchiTun bayan bayyanar bayanai kala kala daga Bakin manyan malamai na cikin kasa Nigeria game da hukuncin saki wanda yan film keyi a cikin shirin film din, inda malamai da dama suka fito kuma suka nuna cewar indai jarumin dake cikin Shirin film din ya ambata ya saki matarsa wacce suke shirin da ita to matarsa dake gida ya saka ba wannan ba indai malamai da dama sukai na'am da wannan maganar yayinda wasu da dama dama sauran mutane gama gari suka nuna rashin gamsuwarsu da wannan hukuncin hakan yasa suka bazama zuwa gurin fa wasu malaman domin sake neman sani, sannan kuma a warware musu tsakanin aya da tsakuwa.

Su malaman da suka ce sakin ya iyu sun fadi hujjarsu yayinda suma wanda suka nuna bata saku ba sun fadi tasu hujjar.

Na saurara a gun wani malami da yake cewa babu saki ga matar da ba'a daura muku aure da ita ba, kaga idan haka ne matar da suka saki a film dama ba aure aka daura musu da ita ba.

To saidai kuma babban malamin wato sheik Dahiru Bauchi yace sakin da yan film suke yi a cikin shiri babu wata alaka da zaisa ace wai mutum ya saki matarsa ta gaskiya har yake cewa ta inda sakin zai iyu daya ne saidai idan shi jarumin da yayi sakin da matarsa ta gaske suke shirin kuma ya furta cewa ya sake ta to wannan kam sakin ya iyu domin babu wasa cikin saki.

To saidai idan bada matarsa suke shirin ba wannan kam babu wani abu.

Allah ne masani

Comments