Min menu

Pages

Tafiyar ceto 2
A bangaren samjid kuwa wadda shi ko yauhe zaka sameshi tare da Jaihan domin sun kasance sa'annun juna ne kuma tazarar dake tsakaninsu ma sati gudane kawai shi yasa suka taso cikin abota da ra'ayi iri daya, shidai samjid gabaki dayansa mahaifiyasa jaida'atu ya biyo wajen faramfaram da jama'a gashi zaiyi wuya ka ganshi yana fushi gashi da matukar saukin kai haka zalika ko yaushe Razik yana tare dashi domin shi Razik ya kasance mutum mai marukar yawaita tambaya shikuwa samjid mutum ne wadda ke bashi hadin kai wajen amsawa. Idan kuma akayi duba izuwa Abtar da Zaffar wannan kam sai wadda ya ganin domin sun kasance babu wani abu dake iya  rabasu face barci kai wani lokacin ma a waje guda suke kwana tsabar shakuwar dake tsakaninsu.

Gidan sarautar kasar farisa ya kasance tafkeke na gaban kwatan domin girman sa yakai babban gari kuma acikin wannan gidama kadai kayi gudu da doki na kusan sa'a goma daga wani ginin zuwa wani ballanta ace kuma  ka karade gidan sarautar to saika kwana ka kuma kana fama baka gama zageye shiba akan ingarman doki. Shidai wannan gida an kawata shi da abubuwa na more rayuwa da manya manyan lambu ta kowace kusuwa kuma an tsara gidan bangare bangare har izuwa uku bangaren sarki da matansa sai bangaren yayan sarki sai kuma bangaren bayin gida wanda ya hada da sashin dakaru. A bangaren tsaro duk wani abu mai sharri koda aljani bai taba bi koda  tasaman wannan gida domin katanga gidan ginanniyace mai kaurin da fadinta yakai kamu dubu  tsawon  zira'i dubi goma.jikin katangar an yabeshi da wani sinadari da ake kira da YENIY.Shidai yeniy sinadari ne dake bada kariya daga kariya daga sihiri kowani Aljani kuma ana amfani dashi wajen yin abubuwa da dama kama layar daure ajani da boye duk wani abu daga wani mai amfani da sihiri wannan shine ya saka wannan gida ko masu sihiri da Aljanu babu wadda yasan sirrinsa.

Idan aka dawo batun jarumtakar yayan sarki saidunnajabi kuwa wannan yafi karfin a misaltahi domin mutum daya ma kadai daga cikinsu yana iya tarwatsa gungun sadaukan yan fashi idan kuma suka hadu suna iya tarwatsa runduna duk girmanta su koresu, wannan tasa ala tilas kowane makiyi nasu ya hakura ya dagawa wannan kasa kafa domin ya rayu cikin zaman lafiya,A  kudu da kasar farisa akwai wani sarki mai suna BARRUM NAJAGARI wanda yake mulki a wata kasa da ake kira BALDA yasha kawowa kasar farisa hari da zummar ya rushe Mulkin sarki saidunnajabi amma abin ya faskara daga karshe saida ya nemi sulhu da wannan yaya nasa cewa bazai sake kaiwa hariba kowacce kasa ba dake nahiyar sannan suka kyale shi kuma suka saka masa takunkumin kar ya kara zuwa kasar su. Amma wannan sarki har yau har gobe babban burinsa bai wuce yaga bayan mulkin sarki saidunnajabi ba amma dole ya hakura ta ciki na ciki domin anfi karfin sa.

Tunda wannan yara suka taso suna kanana sarki saidunnajabi ya sakasu a wata makarantar horon yaki kuma ya dankasu a hannun babban sarkin yakinsa mai suna Sadauki HAZAN da ga marigayi tsohon sarkin yaki kuma aminin sa na kut da kut mai suna RAHJAINI, Haka wadannan yayan sarki suka taso cikin horon yaki ba dare ba rana har suka zama manyan gwarazan jarumai wadda saida suka ciwo manya manyam lambobin yabon daba'a taba cin irin suba wadda kuma zaiyi wuya a samu wadda zaici ko anan gaba a wannan makaranta. Wani abu kuma na musamman dazai dada burgeka a wajen wannan yara na sarki shine bayan iya yaki na gama gari ko wanne daga cikinsu ya kware wajen amfani da wani makami, misali Jaihan wadda shine babba wadda sarcecen kato ne na gaban kwatance ma'abocin murdaddun damatsa da faffadan kirji da fuska ma'abociya siririnta ya matukar kware wajen iya sarrafa takobi koda babu garkuwa a hannunsa haka zalika fada idan har ya kasance da jiki za'ayishi wannan kam ba matsalar sa bace, Samjid wanda ke biye dashi wadda ma'abocin tsayine da dogayen gabobi, mai matukar hasken fata wadda keda damatsa masu kulli kulli saboda matukar murdewa shima wajen wannan fage na iya ammafani da takobi da fadan hannu anan ya kware watakila ko domin alakar dake tsakanin sune da jaihan tasa. A bangaren samira da suhila wanda sun kasance kyawawa wanda kyawansu bazai siffantu ba a wajen mai suffantawa ba saidai kawai ya zana abin dazai iya zanawa akansu sun kasance tamkar taurari wajen haske kyawunsu kuwa ruda duk wani na miji yake kai idan ana bawa makaho labarin kyansu har rudewa yake domin kyawun da suke dashi, Samira da Suhila wadda dama abokan haihuwa ne sun kasance kwararru idan aka zo batun amfani da kibiya domin duk lungu ko  zafin naman halitta cikin sauri harbin kibiyarsu yake cimmasa kuma su biyu kadai sukan iya gigita abokan gaba duk matukar yawansu wani kari kuma shine suna iya sarrafa jikinsu wajen yin tsalle tsalle, Idan kuma muka koma bangaren Zaffar da Abtar kuwa suma abu iri daya suka iya wato  amfani da gatari da kuma duk wani gajeren makami kamar wuka da makaman tansu,sannan kwararrune wajen hada tarko kowane iri ne domin da tarko kadai suna iya kama Aljani su daureshi ba tare daya sami damar tserewa ba, suma kamar samira da suhila sun iya tsalle-tsalle. Shi kuwa Razik wadda shine karami a kaf yayan wannan sarki ya kasance mutum mai matsakaici jiki kuma ba wani murdadde bane sosai baiwarsa da fasahohinsa dabam suke dana kowa da farko shi kwarrarene wajen sanin ilimomi dabam dabam wadda ya samu a wajen manyan masana daya ke ziyarta wuri wuri kuma ya shahara wajen hada sinadaran yaki masu hatsari kala-kala kuma yana da sani akan tarihi da kuma bangarori na duniya gashi da shikima wajen yaki don shi kadai yakan kori runduna ta mayaka wajen saukar musu da kofofin bala'i kala kala. Razik shi ne jarumin da ko Aljani yana tsoransa domin razik shine mutum na farko da a kasar farisa ya gano cewa sinadarin yeniy yana da amfani wajen daure aljani ko hanashi ratsa duk wani bango da aka yabeshi dashi yana da sani akan wannan dama duk wata hanya dashi kadai ya santa duk da haka Razik jarumi ne na gaske kuma yana da matukar naci da juriya wajen yaki duk wahalarsa da masifarsa, Amma duk da haka yan uwansa suna masa kallon yaro ne shi a fannin yaki domin basu gama sanin saba.

A bisa al'ada ta wadannan 'ya'yan sarki sukan fita farautar kwana uku a karshen ko wane wata, kuma suna fara shirin tafiya wannan farauta ne kwana biyu kafin ranar tafiya tazo haka kuma duk lokacin tafiya kowan ne daga cikinsu sai yaje wajen mahaifiyarsa yayi mata bankwana daga bisani sai su hadu a wajen mahaifinsu kana shima suyi bankwana dashi.Yauma dai kamar kullum sun gama shirye-shiryen su tsaf kowa ya nufi sashe da mahaifiyarsa take domin suyi ban kwana. Jaihan,Samira da kuma Razik sune suka fara isa suka nemi iso a wajen ummin nasu wato shabila suka shiga ciki suka sameta a wani narkeken falonta,falon waje ne wadda aka kawatashi da narkakken zinare mai kalar shudi da kore kuma ko ina a cikisa an saka wasu kalar furanni wanda suke fitar da wani irin sihirtatcen kamshi mai daukan hankalin mai jinsa sannan falon an shimfide shi da kilisai kala kala tare da wasu girkakkum kujeru na alfarma masu matukar laushi,haske da kuma kyalli. Su jaihan suka shiga suka gaisa bayan sun gama gaisuwa sai suka sami waje suka zauna suna mai fuskantar ta.Jaihan ne ya fara magana da cewa yake ummin mu munzo ne domin muyi bankwana dake zamu tafi farauta kamar yadda muka saba daga nan shabila ta musu nasiha kamar kullum tana mai ce musu ku kula da junanku kuso juna kada ku yarda matsala ko baraka ta daidaita alakarku don haka ina mai gargadin ku dason juna don wannan shine kawai zaisa ku dawwama cikin karfin giwa da farin ciki har karshen rayuwar ku.sannan kuma ina mai sanar daku bayan kun dawo daga wannnan farauta inaso kuje wajen sarkin yaki Hazan yace yana son ganinku sannan tayi musu albarka da fatan dawowa lafiya su kuma suka mata bankwana suka nufi bangaren sarki domin su hadu anan suyi masa bankwana sannan su wuce.

A bangaren samjid da kaninsa Abtar kuwa bayan sun nemi iso sun shiga wajen da mahaifiayarsu Jaida'atu take zaune a falo suka gaisa sannan suka sami waje suka zauna,shima wannan falo zubin sa da girmansa iri daya ne dana Shabila bambamcin su kawai shine kalar zinaren wannan falo ruwa zumane mai haske hakazalika kujerun kalarsu daya da wannan zinare, bayan su samjid sun zauna Jaida'atu ce ta fara magana da cewa barkan ku mazajen yayana taci gaba dacewa idan har na canka yo ranar tafiya farautarku ce tayi cikin faram faram tare da raha take wannan zance nata domin dama dabi'arta ce yin raha da mowane mutum hatta yayanta haka samjid ya biye mata sukayi ta hira sunayi suna sako Abtar a cikin zancen lokaci-lokaci don shi ba ma'abocin zance bane sosai.Bayan sun gama kafin suyi ban kwana Jaida'atu ta dauko wasu layoyi guda biyu kanana wadda aka yiwa ado da ratsin baki da shudi wadda aka cudanya da sinadarin yeniy ta kowane sahin wannan laya bayan ta mika wa ko wanne sannan tafara bayani da cewa wadannan layo na musamman ne dake bada kariya daga dukkan wani sihiri wadda wani masani dangane da fannonin sihiri aminin baba na ya mallakamin su kuma yace dani dukka biyun aikinsa iri dayane ya kuma yimin bayanin cewa zan sami yaya guda biyu a duniya duk sanda suka kai sama da shekara ashirin da biyar a duniya na basu domin wani dalilin amfani da wadannan layoyi zaizo kamar yadda ya gudanar a bincikensa ya gano bayan yayi mini wannan bayani saina tambaye shi menene wannan dalili kawai cewa yayi dani yayi iyakar binciken sa  domin ya gano ko menene amma abin ya faskara,taci gaba da magana ta me cewa saboda haka inaji a jikina wannan ne lokacin daya kama in baku wadannan layoyi kuma yayi mini nuni da kada ku yarda da duk wani mahaluki ya gane kun mallaki wannan laya domin duk tsananin karfin sihirin halitta bazai gane kun mallaki wannan laya ba har sai idan harku kuka nuna masa kuma tsafi ko sihirinsa bazai taba tasiri akan kuba. Don haka ina mai gargadin ku daku tsare kanku kuma kasance masu hadin kai a koda yaushe, bayan ta gama yi musu bayani sukayi bankwana suka wuce izuwa bangaren sarki domin su hadu da yan uwansu don yin bankwana dashi.

Shi kuwa Zaffar da yar uwarsa Suhila suma bayan sun nemi iso sun shiga bangaren da mahaifiyarsa tasu take suka kuwa yi sa'a suka sameta  a falonta,shima wannan falo iri daya ne dana sauran matan sai dai kayan dake cikinsa sun fi na sauran daraja.

Zanci gaba

Comments