Min menu

Pages

Yadda naga mijina da uwar da ta haife Ni turmi da taɓarya

 

Labarin ya faru da gaske


Na Ga Mijina Da Uwar Data Haifeni Turmi Da Taɓarya

(Da gaske al'amarin ya faru)




Masu karatu wannan labarin da kuke shirin karantawa labarin wata dalibar ɓoye ce data turo mini saƙon neman shawara ta, bayan na karanta kuma na bata shawara, sai na nemi izzininta na rubuta wannan labarin a shafina domin neman ƙarin shawarwari daga masu karatu. Lamari ne da ya faru da ita, ba ƙirƙirar labari bane. Da fatan za a bata shawara mai amfani.


"Mun hadu da mijina ne a shekaran da yazo bautar kasa daga jihar sa ta Gombe, aka turo shi koyarwa a makarantar mu ta mata dake jihar Filato. A nan ne soyayya ya shiga tsakani na da shi.

Mun yi kamar shekaru uku muna soyayya. A shekarar data gabata ne a watan Oktoba aka daura mana aure dashi. Na kuma koma garin Gombe da zama.

Mijina mutum ne mai matukar saukin kai da kuma kula da hakƙoƙin da suka rataya akansa. Don haka ne a kullum ina burin ganin mutuwa ce kadai zata rabamu.

Yana gama karatunsa ya samu aiki a wata ma'aikatar gwamnatin tarayya. Aka kuma barshi ya zauna a nan garin su. Sai dai yakan yi tafiya zuwa Abuja idan hakan ya kama.

Kamar yadda na soma baka labari wallahi tunda muka yi aure har zuwan kamin wannan lokacin mijina bai taba mini wani laifin da yau zan rike shi a zuciya ba. Don haka zaman aure mu abun sha'awane ga duk wanda yasan mu.

Mu biyu iyayemu suka haifa. Ina da babban wana namiji wanda a wani rikici na fada addini aka kashesu dashi da mahaifinmu. Don haka muka rage daga ni sai mamanmu.

Mahaifiyarta yanzu take cika shekarunta na 40 da haihuwa. Macece data sadaukar da rahuwanta ganin nawa rayuwar ya inganta. Ganin yadda 'yan uwan mahaifina suka kwace mana dukiyoyin da suka kama mu gada.

Tabbas mahaifiyarta tana da kyau halitta, idan ba ta maka bayani bazakace ta kai shekarunta ba. Haka mutane da yawa suna mata ganin ba ita ta haifeni ba.

Mijina yana da shekaru 35 da haihuwa ni kuma yanzu nake cika shekaru 24.

Bari na tafi kai tsaye wajen dalilin da yasa na rubuta maka wannan sakon.

Yau sati na uku da haihuwa. Na haifi ɗanamiji. Hakan yasa mahaifita tazo ganin jikan ta inda tace zata yi makwannin biyu a gidanmu.

Da yake a babban gida muke. Mai dakuna uku. Kuma ko wani daki da ba dakinsa yasa bamu da wani fargaba na saukar baki ko wani iri ne.

Akwai mutuntawa tsakanin mijina da mahaifiyarta irin na surikai. Amma ko da wasa ban taba ganin wani alamun da zan zarge su da wani abu ba. Sai dai abunda na ganin da idona a daren jiya shi ne ya sauya mini tunanina gaba daya. Ya sa ni ɗimuwa da damuwa, ba saboda natsuwar da Allah Ya kimtsa mini a wannan lokacin ba da tuni na kashe kaina.


Na tashi tsakar dare ne domin na shiga ban daki, sai na duba naga mijina baya kwance dani, da yake shi jaririn namu gadonsa daban. Hakan yasa nayi tunanin ko ya shiga ban daki ne sai wata zuciya tace mini na shiga dakin mahaifiyarta nayi amfani da bandakinta. Hakan kuwa na yanke shawara.

Ina tura kofar kawai sai naga mijna akan mahaifiyarta yana zina da ita. Na kasa cewa komai kawai sai na dawo cikin dakin mu shiga ban dakin da banyi ba kenan ina kwance a kan gado na rufe fuska ta da mayafi inata kuka.

Sai da aka samu kamar mintuna 30 bayan ganinsu dana yi sannan mijina ya dawo. Na kwanta tamkar ina barci. Ya lallaba ya shiga ban daki yayi wanka ya dawo ya kwanta.

A lokacin ne na soma tunanin wata fura da yake kawo mini duk dare nake sha kamin na kwanta saboda matukar son wannan furan da nake yi. Na fahimci jiya daya kawo ban sha taba wanda wajen sau uku yana tambaya ta ko na sha fura daga karshe dai nace masa na sha. Tabbas a wannan furan yake samini maganin barci idan nayi barci sai ya shiga dakin mahaifiyarta.

Malam a yanzu haka basusan na gansu ba. Kuma saura mako guda mahaifiyarta ta koma. Ganin mahimmancin da dukkaninsu biyu suke a rayuwa ta na kasa yanke hukuncin matakin da ya kamata na dauka. Shi yasa nace ko zan iya samun shawara a wajen ka. Don Allah Malam ka taimaka mini ina cikin mawuyacin jarabawar da zuciya ta bazata iya daukaba idan babu shawaran masana.

Me ya kamata nayi. Ni dai ban taba samun matsala da mijina ba sai wannan. Bani da kuma kowa yanzu a rayuwa ta idan banda waɗannan mutum biyu da suka shigar dani wannan matsalar. Don Allah ina neman shawara. 😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭


To masu karatu musamman daliban mu mata da maza ku taimaka mu kubutar da wannan baiwar Allah ta hanyar bata shawara matakin da zata dauka


Tsangayar malam


Comments