Min menu

Pages

Makomar: Kane, Mount, Rice, Odegaard, Maddison, Firmino, Carvalho, potter, Messi, Bruno Guimaraes, Ugarte

 

Musayar yan wasa a yau ranar Talata makomar: Kane, Mount, Rice, Odegaard, Maddison, Firmino, Carvalho, potter, Messi, Bruno Guimaraes, Ugarte 


Ga kanun labaran 

Tottenham na daf da watsi da tayin Manchester United kan Kane, Firmino zai duba yiyuwar tafiya Madrid, Barcelona na daf da rasa Guimaraes, West Ham, Tottenham da Nice na zawarcin potter, Chelsea ta shiga cinikin Ugarte, Xavi ya tattauna da Messi Wakilin sa Kuma Babansa  ya amince da tayin Al-hilal

Ga cikakken labarin 

Tottenham ta kuduri aniyar yin watsi da yunkurin da Manchester United ke yi na sayen dan wasan gaban Ingila Harry Kane, mai shekaru 29, a wannan bazarar, in da shugaban Spurs Daniel Levy ba ya son sayar wa abokanan hamayyarsa na Premier Dan wasan. (Mirror)


Erik ten Hag yana da kwarin gwiwar cewa zai iya shawo kan dan wasan tsakiya na Chelsea dan kasar Ingila Mason Mount mai shekaru 24 da haihuwa ya koma Manchester United a wani bangare na sake fasalin kungiyar sa a bazara da kociyan ya bukata. (Telegraph)


Bayern Munich ta shirya biyan £95m kan dan wasan tsakiya na West Ham da Ingila Declan Rice, a yayin da kungiyar ta Jamus ta kuduri aniyar doke Arsenal wajen siyan dan wasan mai shekaru 24. (Mirror)


Paris St-Germain na zawarcin dan wasan Arsenal dan kasar Norway Martin Odegaard mai shekaru 24. (Mail)


Tottenham da Newcastle da kuma Arsenal na daga cikin kungiyoyin gasar Premier da ke son dauko James Maddison na Leicester kuma dan wasan tsakiyar Ingila mai shekaru 26 zai iya kaiwa kusan fam miliyan 40. (Mirro)


Crystal Palace ta tuntubi tsohon kocin Chelsea da Brighton Graham Potter kan komwarsa kociyan kungiyar, Nice i tana son dauko dan kasar Ingilan mai shekaru 48. (Foot - in France)


Brighton ta kammala daukar dan wasan tsakiyar Jamus Mahmoud Dahoud, mai shekaru 27,  kyauta daga Borussia Dortmund. (Fabrizio Romano)


Liverpool ta yi watsi da tayin din-din-din daga kasar waje na neman dan wasan tsakiyar Portugal Fabio Carvalho, mai shekaru 21, yayin da kungiyar ta Merseyside ke tunanin bayar da dan wasan mai shekaru 20 a matsayin aro. (Sport  - subscription required)


West Ham ce ke kan gaba a yunkurin dauko James Ward-Prowse, inda Southampton taiwa dan wasan tsakiyar Ingilan mai shekaru 28 Kudi kan fan miliyan 40. (Sun)


Newcastle na da kwarin gwiwar cewa za ta iya daura dan wasan tsakiya na Brazil Bruno Guimaraes, mai shekaru 25, zuwa sabon kwantiragi a St James Park duk da sha'awar da Barcelona ke yi masa. (90min)


Dan wasan gaban Brazil Roberto Firmino, mai shekaru 31, wanda zai bar Liverpool a bazara, yana jiran ya ga inda zai dace da shirin Real Madrid kafin ya yanke shawarar komawa Spain. (Mail)


Kocin Barcelona Xavi ya ce yana tattaunawa da dan wasan gaban Argentina da Paris St-Germain, mai shekaru 35, Lionel Messi, kan komawarsa Camp Nou a bazara. (Standard)


Amma mahaifin Messi kuma wakilin sa Jorge ya amince da yarjejeniyar shekaru biyu da kungiyar Al-Hilal ta Saudi Arabiya kan kudi Yuro biliyan 1.2 (£1.1bn). (Foot  -  in France)


Everton na ci gaba da zawarcin dan wasan gaban Mali El Bilal Toure, mai shekaru 21, bayan komawarsa Almeria a ranar Lahadi. (Mail)


Chelsea ta fara tattaunawa kan cinikin dan wasan Uruguay da Sporting CP Manuel Ugarte mai shekaru 22. (90min)


Sauran 'yan wasan tsakiyar da Chelsea ke zawarcin sun hada da dan wasan Brighton dan kasar Argentina Alexis Mac Allister mai shekaru 24 da kuma dan kasar Ecuador Moises Caicedo mai shekaru 21. (Guardian)


Dan wasan tsakiya na Amurka Brenden Aaronson, mai shekaru 22, yana yunkurin  barin kungiyar tasa ta Leeds kuma ana sa ran zai bar Elland Road a wannan bazarar. (Athletic - subscription required)


Crystal Palace na tunanin tayin aro ga Chelsea kan dan wasan Ingila dan wasan tsakiya na 'yan kasa da shekaru 19 Lewis Hall, mai shekaru 18. (Mail)

Comments