Min menu

Pages

Watsapp Yakara Sabbin Abubuwa 5 Masu Matukar Daukar Hankali

Watsapp Yakara Sabbin Abubuwa 5 Masu Matukar Daukar Hankali
image credit: Google

Watsapp Yakara Sabbin Abubuwa 7 Masu Matukar Daukar Hankali

Kamfanin Meta wanda shine yake da mallakin manhajar Watsapp da mutane suke kara sonta akoda yaushe, yakara wasu abubuwa guda 5 sabbi wanda duk mai amfani da Watsapp zasuyi matukar burgeshi kwarai da gaske. 

Wannan manhaja ta Watsapp tana da muhimmanci a yanzu sosai kuma tana saukakawa mutane wasu abubuwa wanda da ba ita da mutum zai kashe kudi da kuma bata lokaci, ka karanta wannan post har karshe

Abubuwa 5 Sabbi Da Watsapp Yakara

Delete For Me: Masu amfani da manhajar sun san akwai wannan tsari (delete for me) wanda ma'anarsa shine idan wani ya turo sako zaka iya goge shi iya kai kadai amma shi sakon yana nan a wajensa,  matsalar shine ada idan ka goge shikenan yatafi har abada

Watsapp yanzu yabada dama na wasu 'yan dakiku idan kayi Delete For Me zaka iya dawo dashi cikin kasa da minti daya, wani sa'in zaka iya goge sako kuma nan take kaji kana bukatar sa. sai dai wannan tsari iya masu amfani da iOS ne zasu iya morarsa yanzu, amma yana tafe ga masu amfani da Android

Edit Sent Message: Wannan tsari za'a iya cewa zaifi daukar hankalin mutane sosai, kamar yadda ake amfani da Facebook da Telegram yanzu zaka iya editing din sakon daka tura a Watsapp

Hakan zai baka dama idan kayi kuskure acikin sakon daka aika ka gyara nan take, za'a iya cewa wannan tsari wata babbar dama ce manhajar tabawa masu amfani da ita

Call Countdown: Watsapp yana da tsarin video call wanda masu amfani dashi sun san haka, daga yanzu duk lokacin daza kayi video call akwai irge daga 1 zuwa 3 (countdown) daza kagani kafin kiran bidiyon yatafi

Online Status: Wannan tsari yana nufin waye zai san lokacin da kake kan Watsapp wanda dama akwai shi, sai dai yanzu manhajar ta sabunta shi ta yadda zaka iya zabar wanda zasu san lokacin da kake amfani da Watsapp

Import Backup: Wani lokaci yana iya zuwa ka goge sakonnin Watsapp dinka gaba daya, wannan tsari abinda yakawo shine yadda zaka iya dauko sakonni ko wani irine daka adana (backup), amma wannan tsari zai maka amfani ne idan kayi backup din watsapp charts dinka

Karin Bayani: Idan kana son more wadannan sabbin abubuwa dole ka tabbatar watsapp din da kake amfani dashi sabo ne, zaka iya shiga PlayStore domin sabunta manhajar watsapp akoda yaushe, Please Kuyi Share

Comments