Min menu

Pages

wuraren 6 da mata basu isa shiga ba a duniya duk matsayinsu.

 

wuraren  6 da mata basu isa shiga ba a duniya duk matsayinsu.Sau tari mafiya yawan mutane suna yawan faɗin cewa duk abin da namiji yayi mace ma zata iya koma tana iya yin wan da ya fishi, sai dai kash ga wasu zababbun wurare dake wasu ƙasashe a cikin duniya in da a al'adansu   ba'a taɓa barin mace ta shiga, ko kuma mace bata da damar shiga wadannan wuraren saboda yadda gurin yake da mahimmanci tsaro da kuma wasu abubuwa wanda bazai taba iyuwa mace ta shiga wannan gurin ba duk yadda takai da girman matsayinta ko daukakarta.


Dan haka ga jerin wuraren zamu kawo muku daya bayan daya.


1. Ayyappan temple : wani gurine a garin Sabarimala a ƙasar india ba a taba barin duk wata mace indai ta balaga zata iya daukar ciki misali yan shekarun da suka kama daga shekara sha hudu zuwa hamsin ta shiga wannan guri sbda al'adansu.2.Haji Ali  dargha:  Shima wannan wani yanki ne a cikin garin islet of worli a kudancin Bombay na ƙasar India, shi wannan gida wani gurine keɓantacce kuma mai tsarki na tarihi wanda aka haramtawa mata shigan shi saboda suna jinin al'ada3.Mount Athos: shima wani yanki ne a ƙasar Europe wanda maza ma da kyar suke samun yardan shiga gurin, ita ko mace an haramta mata bi ta gurin ma gaba daya balle zama a gurin, ko da zata zauna sai ya kasance tsakanin da gurin kamar kimanin kilomita ɗari biyar, a gurin ko Macen dabba mutum bazai gani ba bare har a bari su rayu ko su zauna a gurin.
4.Mounte Omine: Wani yanki ne a ƙasar japan an ƙirƙireshi lokaci mai tsawo daya shude (8 century)Gurine na al'adun duniya baki daya, Dan haka  ba'a amince kowacce mace ta shiga gurin ba saboda zata iya ɗauke ma mazan gurin hankali.


5.Mlimadji beach: Wani wuri ne a yankin afrika mallakin wasu ƙabila mai suna archipelago wanda aka fi sanin su da Comor island waɗan nan mabiya addinin sun tsaya akan cewa ba wata mace da aka amince mata ta shiga gurin.6.  OKINOSHIMA:wani gurine a ƙasar japan da aka kirkireahi don maza kawai su dun ga zuwa duk shekara suna ziyara.

Comments