Min menu

Pages

Wadi-e-Jinn, wani wajen aljanu a kasar Saudi Arabia 🇸🇦

 Wadi-e-Jinn, wani wajen aljanu a kasar Saudi Arabia  🇸🇦 Menene Wadi e Jinn?


Wadi-e Jinn: Wani Babban Wuri Mai Kyau Kusa da Madina

Wadi Al-Baida, wanda kuma ake kira Wadi Al-Jinn, wani kwari ne mai ban mamaki inda motoci ke tafiya ba tare da direbobi sun Tuka su ba. Kwarin yana da nisan kilomita 30 daga arewa maso yammacin Madina. Yana jan hankalin dubban jama'a da baƙi daga ko'ina cikin Masarautar da kuma ƙasashen waje.mutanen yankin sun yi imanin cewa akwai Aljanu a wurin. Kwarin yana kewaye da tsaunuka a gefe guda uku kuma yana da siffa A zagaye Kamar Kwai. An san shi da Wadi Al-Jinn ko Wadi Al-Baidah.


litattafan Musulunci Da dama sun tabbatar da samuwar Aljanu a cikin kwari. Alqur'ani ya ambaci Aljani sau 29. Yana da labarai da yawa da suka shafe su. An yi imani da cewa su halittu ne Wadanda Basa ganuwa da suke tare da mutane, amma suna rayuwa dabam. An yi su da wuta mara hayaƙi kuma suna iya tashi sama.Mutane da yawa sun tafi don bincika kwarin kuma su fuskanci gaskiyar a labarin da ake ke bayarwa. Matafiya sun tafi can don sha'awar gwada wurin ta hanyar kashe wuta motarsu tare da sanya motar a ( Slow ) Motarsu ta fara motsi,  ta nufi sama, hakan yasa Masu motocin suka rude, An bayar da rahoton cewa motoci na gudun kilomita 120 cikin sa’a ba tare da wani mutum ya tuka su ba.A wannan waje na Wadi Al-Jinn idan aka zuba ruwa a kasa a gangare, sai aga ruwan yana yin sama a maimakon ya Gangare kasa. 


Mutanen yankin da suka kwana a cikin kwarin da daddare sun ce sun ji muryoyin da ke neman su fice. Ana cewa “ku fita daga nan Wannan shine wurinmu, ” sun yi iƙirarin cewa haka muryoyin suke gaya musu.


Duk mai tafiya Saudiyya zai iya ziyartar wurin da ke kewayen Madina don duba abubuwan al'ajabi da ke cikinsa.


Amma A Lura


1, Tafiyar kusan rabin sa'a ce daga birnin madina inda mutane za su ji daɗin kallon yanayi.


2, Wurin ban mamaki na kwari ba shi da wurin zama. Don haka dole ne mutum ya ɗauki abinci da abin sha ya tafi tare da su.


3, Abubuwan da ke faruwa a farkon fitowar rana abin kallo ne a cikin kwarin. Tunda buɗaɗɗiyar  hanya ce, dole ne mutum ya je ta bayan ko kafin azahar don guje wa zafi rana, Idan yanayi yana da kyau, kowane lokaci ya dace don ziyartar wannan kyakkyawan wuri.Comments