Min menu

Pages

Fati Washa itace sumayya a shirin labarina season 5

 Fati Washa itace sumayya a shirin labarina season 5

Shirin labarina zango na biyar zai fara zuwa muku ranar biyu ga watan 9 a channel din Saira movie inda fati Washa itace sumayya a shirin labarina season 5 kamar yadda ta maye gurbin Nafisa Abdullahi.

                   Labarina season 5 

Mutane da yawa dai sun kagu sosai suna ta jiran bayyanar shirin na labarina wanda zaizo daga zango na biyar har zuwa labarina season 6 kamar yadda aka samu sanarwar daga director din shirin Malam Aminu Saira mai kamfanin na Saira Movie.


Shirin labarina shiri ne wanda mutane da yawa suke bukatar ya fito domin ganin yaya zata kaya kamar yadda aka dakatar da shirin a karshen labarina season 4 wanda mutane ke son ganin menene zai faru a zango na biyar din.


A zango na hudu dai kowa ya sani Nafisa Abdullahi itace sumayya, to saidai labarai da yawa sun bayyana cewar jaruma Nafisa Abdullahi ta fice daga shirin labarina, wannan yasa mutane ke ta tambaya ko binciken wacece zata maye gurbin Nafisa Abdullahi a sabon shirin da za'a fara haskawa a zango na biyar?

Sai gashi kwatsam an nuna Fati Washa a matsayin sumayya, wanda babu tantama itace zata maye gurbin nata. 

Labarina shiri ne mai dadin kallo wanda mutane da yawa suke matukar son kallonsa domin mafiya yawa sunce sunfi kallonsa fiye da sauran hausa series din da ake nunawa a yanzu irinsu izzar so da kuma sanda da sauransu.


Koda yake kyawun shirin ya biyo bayan samun kyakkyawan aiki daga mai bada umarnin shirin sannan kuma dama dole yayi kyau domin wanda ya rubuta labarin ya kasance babban marubuci mai hazaga a duniyar marubuta Hausa Novels, dama rubutun fina finai wato Ibrahim birniwa.


Domin ya rubuta hausa novels complete documents, masu yawa lokacinda ake kan rubutun litattafan da kuma karantawa domin ana tunanin hatta labarin nasa wanda aka mayar dashi shirin labarina din wani bangare ne na daya daga cikin littafinsa da yayi a zamanin baya.


Ku kasance da channel din saira movie ranar biyu ga watan 9 domin kallon shirin labarina season 5.

    Labarina season 5 episode 1@arewa24 and Saira movie,, 2_09_2022Comments