Min menu

Pages

Anji karar harbe harbe a garin kiyawa jihar Jigawa

Anji karar harbe harbe a garin kiyawa jihar Jigawa Anajin karar harbe-harbe a garin kiyawa na jihar jigawa a daren nan, sai dai bisa ga dukkan alamu kamar yadda wasu al,ummar garin suka shaida mana cewa akwai hasashen cewa 'yan fashi ne masu karbar kudi a hannun al,umma suka shiga garin a daren nan.. 


Dama dai irin wadannan barayin sun saba zuwa wasu daga cikin garuruwan na jihar suyi barna.


Kamar yadda muka samu rahoton harbe harben saidai ba'a tabbatar da mutane nawa ne suka rasu ba.


Tuni dai wasu daga cikin kasuwannin da suke ci a kusa da garin suka watse kowa daga cikin mutanen suka kama gabansu..


Comments