Min menu

Pages

Wasu yan biyu ( Tagwaye ) sun auri mata daya kuma sunce suna jin dadin zama da ita.

 Wasu yan biyu ( Tagwaye ) sun auri mata daya kuma sunce suna jin dadin zama da ita.


Abin mamaki dai gaskiya baya taba karewa a wannan duniyar, kuma kullum labarai na mamaki da al'ajabi sai dada faruwa suke wasu idan mutum yaji zai dade yana tunanin abin yayinda wani abin kuma idan mutum ya gani ko yaji maimakon ya bashi mamaki ma saidai ya bashi haushi da takaici.


A yau cikin shirin namu muna tafe muku ne da labarin wasu tagwayen samari ma'ana yan biyu da suka auri mace guda daya kuma suke zaman aure tare da ita cikin soyayya da kwanciyar hankali.


Abin kam kwarai da mamaki ace maza biyu sun auri mace guda to amma su wadannan tagwayen sunce hakan da sukayi daidai ne domin suna son matar tasu kuma suna jin dadin zaman aure da ita.


Kamar yadda labari yazo daga gurin marie Josiah  matar yar kasar Rwanda data auri tagwayen maza biyun tace da farko da dayan ta fara haduwa kuma bai fada cewar yanada dan uwa guda daya da suke a matsayin tagwaye ba.


Matar me suna Marie ta sake cewa kafin abin ya faru basu taba zuwa shira tare ba, a ranar da suka hadu tare kasa gane su tayi domin kai tsaye gurin dayan taje ta sumbaceshi ta dauka shine wanda suke soyayyar ashe bata sani ba bashi bane.


Shima sai dayan yaje ya sumbace ta sai a lokacin suka fahimci abinda yake faruwa tun daga lokacin suka fara yanke shawarar kulla alaka mai karfi tsakanin su.


Ba'a samu wata matsala ko tangarda ba daga wajen wadannan yan biyun na cewar zasu auri mace guda daya haka ma bayan anyi auren.
Haka suka ci gaba da zama da matar tasu guda daya cikin kwanciyar hankali duk da sun samu kalubale daga gurin jama'a amma haka suka toshe kunnuwansu.


Babu wata damuwa suka zauna zaman lafiya ba tare da wata damuwa ba har tsawon lokaci

Ku kalli bidiyon nasu anan

Comments