Min menu

Pages

Wani rami wanda yayi shekaru 50 yana ci da wuta

 Wani rami wanda yayi shekaru 50 yana ci da wuta 



Akwai wurare masu matukar bada mamaki da al'ajabi a wannan duniyar wanda kuma ya kamata su zama izna ga mutanen dake rayuwa a cikin Duniyar.

Abubuwan sun isa duk wani dan Adam yai nazari kuma yayi tunanin cewa wannan duniyar fa akwai wanda yayi ta kuma shine yake da ikon juyata wato Allah kenan madaukakin sarki.

Allah shine yayi duniya kuma ya shimfida kasa sannan yayi abubuwa da yawa a cikinta kamar tsaunuka koguna da sauran abubuwa sannan yayi su kala kala.

Daga cikin kogunan akwai wanda suke tafasa sannan akwai wanda launinsu kala kala ne sannan akwai wanda idan mutum ya taba ruwansa ma take zai daskare ya zama kamar Dutse

Yau cikin abubuwan da Allah madaukakin sarki ya zuba a cikin duniya munzo muku da labarin wata sahara  Mai suna davaza wanda a cikinta akwai wani rami mai girman gaske wanda wata azababbiyar wuta take ci sannan take fitowa daga cikinsa.

Wannan gurin ya bawa Duniya baki daya mamaki  ta yadda wuta mai tsananin zafi take fita daga wannan Ramin.

Wutar ance tana ci fiye da shekara 50 kuma har yanzu bata mutu ba


Wannan waje ne da dubban mutane sukan je daga kasashe daban daban domin gani, har wasu da dama suke cewa Kofar Wutar Jahannama ce, wacce take dauke da wasu abubuwa na ban mamaki wanda hakan yasa aka koma kiran wajen da suna "Gate of Hell" ko kuma "Door of Hell".

Daga cikin abubuwan mamakin wannan gurin shine ruwan sama baya kashe wannan wutar

Sannan akwai iskar gas mai karfi da take fitowa daga cikin Ramin

Zafin gurin yana kaiwa degree dubu da doriya na ma'aunin yanayin zafi, sannan wani lokacin yana yin kasa da degree 48.

Zafin gurin yana kaiwa nisan fin kilometers 80.

Duk lokacinda zafin ya furo yana yin awun gaba da duk wani daya kusanci wajen walau mutum ko Dabba.

Har yanzu dai mutane da masu bincike sun gaza gano ta inda wutar take bare har asan hanyar da za'a iya kashe ta.

Kungiyoyin duniya sun hadu akan haka amma abu yaci tura.

Gate of hell sunan gurin kuma yana  kasar Turkmenistan, wacce ta fada yankin kasashen Rasha a yanzu, ada karkashin Tsohuwar Tarayyar Soviet take.



Comments