Min menu

Pages

Wani gari wanda basa aurar mace idan har ta taba zina kafin aure

Wani gari wanda basa aurar mace idan har ta taba zina kafin aure.
Idan har kin taba zina to baza ki auru ba a wannan garin.Wannan wani babban darasi ne ga duk budurwar data rasa budurcinta, saboda yadda take tafiyar da rayuwarta ko kuma yadda take kula maza, inda idan aka tabbatar da yarinya budurwa ce hakan yana sawa ana girmamata sannan ana ganin mutuncinta da kuma martabar iyayenta.


Haka kuma idan mace ta kasance wacce ta taba zina zata zamto abar kyama da kuma zagi a gun mutanen wannan kauyen wanda hakan zaisa ta rasa wanda zai aure ta.
Wani gari a cikin kasar south Africa suna gabatar da gwaji a shekara sau biyu ga yan matansu domin a tabbatar da yarinya a matsayin budurwa.

Duk yarinyar da aka samu budurwa ce ana bata certificate na shaidar ita budurwa ce, wacce kuma aka gano ba budurwa bace shikenan ta shiga a uku domin za'a ringa nunata ana tsangwamarta a gari.

A kwanakin baya an nuna yadda ake gwada yan mata a wani gurin bauta a wannan kasar ta south Africa harma ake bawa yan mata shaida ( certificate ) idan har aka tabbatar da cewa mace bata taba yin zina ba, wanda wannan ya jawo maganganu a kafafen yada labarai.

Sannan kabilar zulu ma suna gabatar da wannan al'adar 

Wannan abun da ake wasu sunji dadinsa wasu kuma basuji dadinsa ba 

Comments