Min menu

Pages

Turawa sawa yan Africa takunkumin karfe ne idan suka kamasu a matsayin bayi saboda wadannan dalilan

 Turawa sawa yan Africa takunkumin karfe ne idan suka kamasu a matsayin bayi saboda wadannan dalilanHakika an cutar da yan Africa ta bangarori da yawa lokacinda turawa suka shigo Nahiyar suna kamamu a matsayin bayi.

Sun horar damu da nau'ikan abubuwa masu matukar yawa.

Daga cikin abubuwan da suke wa yan Africa idan suka kamasu harda sanya musu takunkumin karfe wanda shi suna sanyashi ne saboda wadannan abubuwan.

1 Domin su hana bayin da suka kama cin yayan itatuwa kamar su apple, lemo, ayaba, abarba da sauransu a lokacinda suke musu aikin nomansu ko kuma gyaransu a gonakin da suka kwace a hannunsu.

2 Domin su hana yan African da suka a matsayin bayi rera dadadan waking da suke gabatarwa da yarensu, da kuma irin wakokin da suke masu nuna an cutar dasu ko kuma ana kuntata musu wanda hakan yake sanyawa wasu daga cikin bayin kokarin yin tawaye.

3 Domin hana bayin da aka kama koyawa yayansu yin daddadan yarensu da suka gada tun iyaye da kakanni wanda wannan yasa da yawa daga cikin wanda suka taso din basu iya daddadar magana ta asali ba.

Muna ji muna gani suka hanamu yarenmu suka cusa mana yarensu da dabi'a irin tasu


Comments