Min menu

Pages

Kofar da idan aka fice ta cikinta ba'a dawowa ( The door of no return )

 Kofar da idan aka fice ta cikinta ba'a dawowa ( The door of no return )Wannan wata kofa ce wacce idan mutum ya fice ta ciki bazai taba dawowa ba ya tafi kenan ( The door of no return) sunanta.


Kofar tana kasar Senegal a tibirin goree, mafiya yawan yan Africa sunbi ta cikin wannan kofar hannu da kafarsu daure da sasari inda turawa suka dauke su a matsayin bayi shekaru 400 da suka wuce .

Duk lokacinda ka fice ta cikin kofar nan to shikenan kayi bankwana da yan uwanku da sauran danginku.

Gaba daya rayuwar mutum ta baci ya zama bawa kenan a gurin turawa, domin ta wannan kofar sukai ta ficewa da mutanen da suka kama a matsayin bayi a wancan lokacin.


Wannan dalilin yasa aka sanyawa wannan kofar door of no return.


A zamanin baya kam turawa sunyi mana mulki yadda suka ga dama 

Comments