Min menu

Pages

Kasar da ake ginawa budurwa daki a waje tana kwanciya da samari harta samu wanda yayi mata ta aura

Kasar da ake ginawa budurwa daki a waje tana kwanciya da samari harta samu wanda yayi mata ta aura Akwai tarin abubuwan mamaki musamman cikin kabilun dake Duniya domin idan wasu sukai wani abun sai mutum ya dauka ba kansu daya ba.

Mu a Nigeria duk wata budurwa tana iya bakin kokarinta ganin ta kare budurcinta har zuwa lokacinda zatai aure dan hakan shine abin so har a gurin mazajen da zasu aura, to amma a kasar Cambodia su abin ba haka yake ba.


Dole sai yarinyar tayi tarayya da samari masu yawan gaske kafin ta fitar da wanda take so a cikinsu.

Daga yarinya ta girma takai budurwa yan gidansu zasu gina mata daki a waje ita kuma samari zasu dinga kawo mata ziyarar kwana suna kwanciya da ita, duk wanda yafi mata a cikinsu shi zata zaba ta fitar a matsayin wanda zata aura.

Suna yin haka ne domin su a dokarsu duk yarinyar da tai aure tofa shikenan mijinta bazai taba sakinta ba duk wuyar yanayin da zasu shiga, wannan yasa suke wannan al'adar na kwanciya da tarin samari dan mace ta samu wanda zata iya rayuwa dashi.

Mu kasance tare daku a wani sabon shirin.

Comments