Min menu

Pages

Wani wanzami wanda yake amfani da gatari wajen yin aski da gyaran fuska

 Wani wanzami wanda yake amfani da gatari wajen yin aski da gyaran fuskaWani dan kasar Kenya mai suna Julius Mwangi ya kware sosai wajen yin aski da kuma gyaran fuska da gatari.

Kowa dai ya sani gatari wani abu ne da ake amfani dashi wajen saran itace ko wasu abubuwa, domin kowa ya sani babu wani guri da za a ajiye gatari a shagon aski domin ba gurinsa bane.

To amma duk da haka an samu wani wanzami da yake amfani da gatari wajen yin aski ga customers dinsa a kasar Kenya.

Julius Mwangi yanada wani shagonsa da yake aski anan Thindigua kiambu, na kasar Kenya wanda yake gabatar da aski tare da gyaran fuska da gatari, kuma abin mamaki yana yin aikin nasa cikin kwanciyar hankali sannan yana samun customers sosai da sosai.


Ga bidiyon wanzamin da kuma yadda yake amfani da gatari wajen yin askiComments