Min menu

Pages

Manyan mutanen da suka taimakawa Janar Sani Abacha ya saci Dala miliyan 23 a kasar waje

 Manyan mutanen da suka taimakawa Janar Sani Abacha ya saci Dala miliyan 23 a kasar waje



Hukumomin kasar Birtaniya sun gano wasu makudan Dalolin da ake zargin Sani Abacha ya sata.


Binciken da aka yi ya nuna kamfanin Mecosta Securities Inc ya saci sama da Dala miliyan 20 a Turai.


‘Ya ‘yan Janar Sani Abacha da wani na-kusa da dangin sun taka rawar gani wajen wannan badakala.


  Kwanan nan hukumar National Crime Agency (NCA) mai binciken laifuffuka a kasar Ingila ta gano wata badakala da dangin Sani Abacha suka tafka. Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Alhaji Mohammed Sani Abacha ya hakura da wani kamfaninsu mai suna Mecosta Securities Inc a Birtaniya. Binciken da aka yi ya nuna cewa wannan kamfanin tsaro na Mecosta Securities yana da akawun a wani bankin Landan, inda a nan ne aka bankado kudin sata.




 A Oktoban 1995 aka bude akawun a wannan banki a Ingila domin a ajiye dukiyar kamfanin. Daga baya, an gano an rika amfani da asusun wajen satar miliyoyi. Wanda yake kula da asusun bankin kamfanin shi ne Sanata Atiku Abubakar Bagudu. A halin yanzu gwamna ne a jihar Kebbi kuma babba a jam’iyyar APC.




 Atiku Abubakar Bagudu

 Jaridar ta ce a cikin wadanda suke kula da kadarori da dukiyar da Sani Abacha da iyalinsa suka sata, takardu sun nuna babu kamar Gwamna Atiku Abubakar Bagudu.


  Binciken da hukumomi irinsu Transparency International suka yi ya nuna iyalin Abacha da na-kusa da shi sun saci kusan Dala biliyan biyar tsakanin 1993 da 1998. Gwamnan Kebbi, Sanata Atiku Bagudu.


 


Mohammed Abacha

Sabon binciken da aka yi ya nuna kamfanin Mecosta ya boye Dala miliyan 21.7 a babban bankin nan na Standard Bank da ke kasar Ingila da sunan Mohammed Abacha. Haka zalika wannan kamfani yana da akalla dala miliyan 1.6 da ake zargin kudin sata ne da aka ajiye a HSBC. An yi wannan ne ta karkasin ‘dan tsohon shugaban kasar. Alhaji Mohammed Abacha 'dan siyasa ne wanda ya taba neman takarar gwamna a jihar Kano. Kafin a buga wannan rahoto, jaridar ta nemi jin ta bakin Gwamnan na jihar Kebbi, amma bai yarda ya ce komai ba. Shi ma Mohammed Abacha bai amsa wayarsa ba. 




Badakalar rijiyar Malabu

 Kwanaki aka ji labari Mohammed Abacha yace ya yi amfani da sunan Mohammed Sani wajen samun rijiyar OPL 245. Abacha ya bayyana haka da aka shari’a da shi a kotu. ‘Dan siyasar yace an cire sunansa daga kamfanin Malabu Oil and Gas a lokacin da yake gidan yari. Da farko Janar Sani Abacha ne yake da 30% na hannun jari a rijiyar man.

Comments