Min menu

Pages

Ƙabilar Da Uwar Amarya Ke Ƙwanciya Da Ango Domin Gwada karfinsa kafin a daura aure

Ƙabilar Da Uwar Amarya Ke Ƙwanciya Da Ango Domin Gwada karfinsa kafin a daura aureKabilar ankole

Shekaru da yawa da suka wuce, tun cikin karni na goma-sha-biyar (15), al’umar masarautar Bantu, da ake kira da “Ankole” – da take son zaman lafiya; kuma mutane ne masu riko da zumunci – sa’annan kuma suna da dukiya ta dabbobi, musamman ma Shanu.


Kabilar Ankole – wadanda ana kiran su kuma da Banyankole, ko kuma Manakole, suna zaune ne a yankunan Mbarara; da Bushenyi; da Ntungamo; da Kiruhura; da Ibanda; da kuma Isingiro – duk a can yammacin kasar Uganda.


Wannan kabila ta Ankole, ko kuma Banyankole, sun kasance suna da wata al’ada ta daban da suke yi duk lokacin da za su aurar da yayan su mata ada can baya – kafin a rusa ta.


A al’adar su kabilar Ankole, da yarinya mace ta cika shekaru takwas (8) cif, za’a fara killace ta a gidansu; ana koya mata yadda za rika kula da miji; da kula da kan ta; za’a rika nau’in baabinci masu gina jiki da suka hadar da: gero; da madara – domin ta ginu sosai.


Ankole, a tsarin su, ba’a so a rika ganin mace siririya – wacce ba ta da nama. Kuma a wannan shekarun takwas da yarinya ta cika, iyayen yarinya za su haramta mata yawan shige-da-fice na ba bu gaira; ba bu dalili, ko kuma aikata duk wata mu’amala da namiji – har ma akan tsoratar dasu da kasha su, idan basu ji ba.


Daga lokacin da akace mace ta kawo shekarun aure kuwa, namijin da zai aure ta; zai kawo Shanu goma gidansu; da Akuyoyi da kuma burkutu a matsayin toshi. 


Wadannan mutane, suna matukar martaba lamarin budurcin mace, da kuma ba shi kariya sosai – domin shine dalilina da yake sanya wa suna killace yaran su mata idan sun kai shekaru takwas din – kamar yadda na ambata a baya.


Haka nan, sabida zumuncin da suke dashi – idan auren yarinya ya zo, duk da irin horon da suke baiwa yayan na su; sai a samu daya daga cikin yayye ko kannen uwar amaryar da za’a aurar, taje wurin wurin angon; suyi lalata – a matsayin gwajin karfi da kuzarinsa; sa’annan a matsayin gudumawa ga amarya.


Wannan kwanciya da yaya ko kanwar mahaifiyar amarya za tayi da sabon ango, abinda ta gani; ko taji – shine za ta kai rahoto gida…kan yana da himma ko akasin haka; yana da lafiya ko bas hi da lafiya; zai iya rike aure ko ba zai iya rikewa ba – duk za taje ta kai rahoto tsaf.


Haka nan, wannan yaya ko kuma kanwar amarya, yana daga cikin aikin ta; ta tabbatar da cewa amaryar budurcin ta yana nan daram – ta hanyar shiga dakin da ango zai fara Tarawa da amarya ayi komai akan idanun ta; ko kuma ta makale a bayan labule; tana sauraron abinda yake wakana a cikin garka.


A garin kuma, uba shine yake nemowa dan sa mata, kuma shine yake biyan duk wani kudin neman aure – sa;annan ana kaiwa wadannan shanun da akuyoyi da kuma burkutu – kai tsaye, sai a fara hidimar biki. 


Amma wannan al’ada ta kwanciya da yan’uwan mahaifiyar amarya key i da sabon ango tuni aka daina ta – sabida mummunan kamu da cuta mai karya garkuwar jiki tayi masu.


Yo dama, ina ni; ina neman aure a wannan gari. Sabida duk wacce ka aure – to yay ace ko kanwar uwar wata amaryar, sabida haka, kana zaune za’a ce maka matar ka taje kauye, ana auren yan yayar ta ko kanwar ta – kuma ka san sauran.Comments