Min menu

Pages

Yan arewa na neman abi musu hakkin matar da yan IPOB suka kashe da yayanta hudu a Anambara

 Yan arewa na neman abi musu hakkin matar da yan IPOB suka kashe da yayanta hudu a AnambaraTun faruwar wannan al'amarin na kashe mata Mai ciki tare da yayanta hudu da akai a Anambara yan arewa suka fara neman abi musu hakkin matar.


Matar da aka kashe ance yar jihar Adamawa ce dake Nigeria taje ziyara ne jihar ta Anambara wani kauye shine wasu daga cikin yan IPOB din suka kashe ta.


Tuni dai yan arewa masu kishi sun fara maganganu masu daukar hankali game da abinda akai ga wannan mai ciki tare da yaya hudu.

Sannan kuma yan arewan sun fara kalubantar duk wasu manya masu fada aji da suka ja bakinsu sukai shiru tun lokacin da abin ya faru ba tare da sunce komai ba har yanzu.

Suna kuma sake kalubantar su akan cewa sune sukai ta yin Allah wadai a yan kwanakin nan lokacin da wata mai suna Deborah tayi batanci ga fiyayyen halitta Annabinmu.


A karshe dai yanzu social media ta rikice, yan arewa na dakon jiran abi hakkin matar da aka kashe tare da yayanta a Anambara


Duk wani dan arewa dan Allah mu tashi tsaye da rubutu akan wannan har ganin anbi mana koken da mukai domin bai kamata ba.
Comments