Min menu

Pages

Wani guri a Africa wanda duk bil'adaman daya je gurin baya taba dawowa.

 Wani guri a Africa wanda duk bil'adaman daya je gurin baya taba dawowa.Akwai gurare na ban mamaki dake cikin nahiyar Africa wanda idan mutum yaji labarin su sai ya cika da al'ajabi saboda yadda wadannan abubuwan suka wanzu, kasancewar Nahiyar Africa babbar Nahiya ce data tara dimbin abubuwa na daga halittun ruwa dana kan tsandaurin kasa.Wasu abubuwan idan an fade su mutum zai dauka ba gaskiya bane saboda yadda suke wajen bada mamaki, misali kamar wani kogi a kasar Tanzania wanda ake kiransa da suna natron, wanda shi wannan kogin duk wata halitta indai tanada rai to idan ta taba ruwan cikinsa take zata daskare ta zama kamar Dutse.

Dan haka yau ma muka zo muku da labarin wani guri duk dai a cikin Nahiyar ta Africa wanda shi wannan gurin duk wanda ya taka kafarsa gurin tofa ya tafi kenan domin bai isa ya dawo ba kuma baza a taba jin koda duriyarsa ba.

Wannan gurin sunansa tafkin Turkana ko kuma lake turkana da turanci a cikin wannan gurin akwai wani guri mai kama da tsibiri ko kuma fasashshen Dutse dake cikin wannan ruwan.

Anyi ittifakin duk wata halitta idan taje wannan gurin shikenan ta tafi saidai wata domin babu ita babu dawowa shikenan sun bata bat, kuma an kasa sanin dalili na batan duk wani daya dora kafarsa a wannan gurin, wannan gurin a kasar kenya yake a cikin ruwan turkana.Akwai wasu turawa a shekarun baya da suka daura damarar zuwa gurin domin yin bincike amma tsawon shekaru babu su kuma babu labarinsu.


Comments