Min menu

Pages

Shege ka fasa, yan kungiyar IPOB sun maida martani.

 Shege ka fasa, yan kungiyar IPOB sun maida martani.Tun faruwar wani mummunan al'amari na kashe wata mata mai ciki da yayanta hudu da yan IPOB sukai a Anambara, wanda hakan ya jawo hankulan duk wasu yan arewa suka fara tofa albarkacin bakinsu na ya kamata a nemowa wannan matar da aka kashe da yayanta hakkinsu.


Mutane yan arewa da yawa sunyi maganganu musamman  a kafafen yada labarai, haka kuma wasu daga cikin malamai ma sunyi bayanin rashin adalci da yan wannan kungiyar ta IPOB sukayi.


Wasu kungiyoyin arewa da dama sunyi magana akan hakan, to amma suma yan IPOB din sun maida martani suna cewa yan arewa shege ka fasa idan basu suka fasa daukar mataki.


Wannan abin da yake faruwa dai wani abu ne wanda sai anyi da gaske ko kuma a barke da tashin hankali mai yawan gaske.

Comments