Min menu

Pages

Jerin kasashen musulmi 9 da suka goyi bayan kafa kungiyar kasashen musulmi (Muslim United Nation )

 Jerin kasashen musulmi 9 da suka goyi bayan kafa kungiyar kasashen musulmi (Muslim United Nation )
 Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana sunayen wasu daga cikin kasashen musulmin Duniya wadanda suka bashi goyon baya domin kafa sabuwar majalissar dinkin Duniya ta kasashen musulmi wallah, wata kafar yada labarai da ke watsa shirye shirinta a kafar sadarwar Internet, ma suna Turkish News ta ce.


 “Wata majiya mai karfi daga fadar shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ta tsegunta mata cewa shugaba Erdogan ya bayya wasu kasashen musulmin Duniya na goyon bayan Mr, Erdogan a yunkurin da yake yi na kafa wata sabuwar majalissar dinki duniya mai suna Muslim United Nation (MUN ).


 Ga jerin kasashen da suka goyi bayan shirin kamar haka, kamar yadda shugaban na Turkiyya ya bayyana.


 Palasdin: “Kafa sabuwar majalissar dinkin Duniya wacce za ta kunshi kasashen musulmi zalla, zai taimaka mana wajen samun yancin kan kasar mu”


 Iran: “Shirin yana da kyau don zai kawo karshen danniyar da Amurka, ke yiwa kasashen musulmi”


 Tunisia: “Zamu bada duk wata gudun mawa don tabbatar da wannan kuduri”


 Iraqi: “Yunkurin abu ne mai kyau kuma muna goyon baya”


 Oman: “Idan hakan zai kawo hadin kan musulmin Duniya to muna maraba da shirin”


 Qatar: “Muna fatana Allah ya tabbatar da wannan kuduri namu”


 Jordan: “Zamu taimaka da duk abinda ake bukata don cimma wannan kuduri”


 Bahrain: “Kasar mu tana maraba da wannan mataki”


 Algeria: “Muna fatan wannan majalissar kar ta zama kamar ta hadin kan kasashen larabawa wacce bata tabuka komai”


 Wadannan sune jerin kasashen da suka goyi bayan wannan kuduri na mu a wasikun da muka tura musu wannan ce irin amsar da suka bamu, amma sauran kasashen da muka tura mawa har yanzu basu maido mana amsa ba, in ji Mr Erdogan.

Comments

2 comments
Post a Comment
  1. Aslm, Dan Allah Inason numbarka, inasonyin magana dakai ne idan babu damuwa

    ReplyDelete
    Replies
    1. Mai kake bukata da kake son number wayana?

      Delete

Post a Comment